Wednesday, November 27, 2013

DR ALIYA ADAMU AHMADDr Aliya Adamu Ahmad na daya daga cikin matasan mata manazarta a Nazarin Hausa. Ta samu digirinta na farko da na biyu daga Jami'ar Usmanu Danfodiyo Sokoto. Ta kuma samu digirinta na uku daga Jami'ar Bayero ta Kano. Ta koyar a Shehu Shagari College of Education Sokoto. A halin yanzu tana koyarwa a Sokoto State University, kuma ita ce shugabar Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya. Taken aikin digirinta na uku shi ne: “Rupert Moultrie East: Gudummuwarsa ga Adabin Hausa, da Kuma Sharhi Kan Ayyukansa”. Ta kuma gabatar da makalu a tarrurruka da dama. An kuma buga wasu takardunta a mujallun ilmi da littattafai. A shekarar 2012 ta je SOAS ta Jami'ar London inda ta yi zaman bicike a matsayin Leventis scholar. Tana da aure da yaro.