Monday, October 19, 2009

NASIRU G AHMAD YANAWAKI

An haifi Nasiru G. Ahamd a unguwar ‘Yan Awaki cikin Birnin Kano, ran 6 ga Safar, 1384, BH. (4/2/1964). Bayan karatun Alkur’ani, ya yi makarantar Firamare Islamiyya ta ‘Yan Awaki, daga 1975-1981. Ya wuce zuwa makarantar Nazarin Addinin Musulunci mai zurfi ta Shahuci (1981-1985). Sai Makarantar Nazarin Shari’ar Musulunci ta Aminu Kano, (1986-1989) inda ya samu diploma a Harsunan Hausa da Larabci da Nazarin Addinin Musulunci. Daga (1993-1996), ya je Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo ta Sakkwato, inda ya samu digirin farko a harshen Hausa.
A shekarar 1984, ya halarci ajin koyon buga keken rubutu (Typewriting) da ke karkashin Hukumar Yada Ilimin Manya ta Kano, a 1992, ya halarci wani kwas da Jami’ar Musulunci ta Madina ke shiryawa, don horar da malaman Arabiyya da addinin Musulunci, a Jami’ar Bayero ta Kano. A 1992 din dai, ya je wani kwas na addinin Musulunci, a garin Idah, cikin jihar Kogi. A 1999, ya yi wani kwas na karatun gida, karkashin “Sincere Writers Club”, inda ya samu takardar shaida (certificate) kan aikin jarida.
A 1991, ya je jihar “Cross Rivers” inda ya yi aikin jami’i mai duba Malaman Kidaya (Supervisor). Ya koyi sarrafa na’ura mai kwakwalwa a aikace, (Practical) a “Urgent Computers” inda ya taba yin aiki. Yana cikin masu duba wakar Hausa, ta jarrabawar ‘W.A.E.C.’ Wakili ne na jaridar “People And Events”. Editan littattafai ne mai zaman kansa. Ya yi aikin koyarwa a makarantu da dama, (Firamare da Sakandare) tun daga 1984 zuwa yanzu. Yana da sha’awar ziyarce-ziyarce da kulla abota, da karance-karance a kowane fannin ilimi da rayuwa. Ya rubuta litattafai da dama, da wakoki jingim. Nasiru kuma na cikin Sahún gaba na ‎ ‘yan Kungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA) reshen jira Kano. A halin yanzu yana karatun digirinsa na biyu a Jamiár Ahmadu Bello (ABU) Zaria.

No comments: