Saturday, May 2, 2009

KABIRU YUSUF ANKA


A wata na karshen shekarar Milladiya ta 1979 aka haifi Kabiru Yusuf Anka a ranar Litinin 1 ga watan Disamba, 1979, a lissafi yanzu yana da shekaru 29 kenan a raye a duniya.
Haka nan ya fara da karatun Alkur'ani a bangaren ilimin Arabiyya kenan wanda idan aka hada da makarantar Islamiyya ta Sabilul Rashad da ke Gyadi-gyadi da Mukhtariyya Islamiyya da ke Fagge da kuma Thimarul Qur'an (bangaren dare) ya sami saukar Kur'ani da sauran tarin littattafan Fiqh, Sirah, Nahwu, Tajwid, Hadis da sauransu.
Ya yi karatun Firamare a Kurna Special Primary School, dake kan titin Katsina daga nan sai ya wuce karamar sakandire ta JSS Kurna, da kuma makarantar GTC K/Nassarawa. Bayan kammalawa ya wuce School of Technology, Kano inda ya sami shaidar satifiket a bangaren Electrical Electronic. Ya kuma wuce Jami'ar Bayero ya sami shaidar Diploma a bangaren aikin jarida (Mass Communication)
Sha'awar sauya layi a karatu ya sa ya koma makarantar sakandire ta Kwakwaci inda ya yi jarrabawar NECO a 2006.
Ya samu shaidar karatun Diploma a bangaren na'ura mai kwakwalwa (Computer) a makarantu biyu: Online Computer da kuma Hands-On Computer Institute inda ya karanci (Desktop Publishing da Data Processing and Maintainence)
Kabiru ya kware a wajen sarrafa na'ura mai kwakwalwa musamman a bangaren zane da bugu (design graphics and typing) wanda har shaidar satifiket ya samu a Mavis Beacon Typing Institute a May 5, 2003 da maki 92% (accuracy)
Haka nan ya buga littattafai, jaridu da mujallu masu yawa a bugun kwamfiyuta, ya kuma tsara shafukan mujallu da jaridu da kuma tsara bangwayen littattafai da yawa.
Marubucin yana da sha'awar aikin jarida da rubuce-rubucen jarida, don haka ya yi aiki a jaridu kamar haka:-
Wakiliya -(mujallar Marubuta) - a matsayin mataimakin Edita.
Inuwar Marubuta -(mujallar Marubuta) - marubuci na musamman
Suda -(mujallar 'yan fim) - marubuci
Kwallon Kafa -(mujallar labarun wasanni) -mataimakin Edita.
Muryar 'Yanci -(jaridar labaran karamar hukumar Fagge) -Edita
Masoya -(mujallar Labaran rayuwa da soyayya) - Edita
Kakaki -(mujallar kare ra'ayin karamar hukumar Fagge) -Edita
Haka ya yi rubuce-rubuce da dama a jaridu da mujallu na kasar nan.
A bangaren kungiyoyin marubuta, Kabiru yana cikin wadannan kungiyoyi:-
Hausa Authors Forum (HAF) -Mataimakin Shugaba
Association of Nigerian Authors (ANA) Kano - a matsayin sakataren yada labarai na bangaren Hausa (P.R.O. Hausa)
Shugaban Gimbiya Publishers.
Kabiru ya fara rubuce-rubucen sa tun yana makarantar Firamare aji na hudu, inda shi ne mataimakin shugaban aji, kuma shi ke karanta littattafan Hausa, kamar irin su Magana Jari Ce da sauransu. Wasu daga cikin littattafan da ya wallafa da sunan shi Kabiru Yusuf Anka sune:-
1. Karfin Hali...
2. Shure-shure...
3. Ninkaya
4. Alwashi
5. Bilkisu
6. Firgita Samari...
7. Rayya
8. 'Yan mata...
9. Kushewar Badi...
10. Salo
11. Hadarin Kaka (a daidaita sahu)
12. Launin So
13. Mataye
14. Rauni
15. Rayayye
16. Dansanda..
A bangaren Turanci ya wallafa:-
1. Standard Dictionary/Teach-yourself *
2. Successful Dictionary/Teach-yourself *
3. An Essential Way of Learning English *
4. Learning English
5. My Pen and Others Stories
*ma'ana da hadin gwiwar wani suka wallafa
Haka nan ya wallafa wasu littattafan da sunan Muhammad Matashi Fagge kamar:-
1. Kalmar So
2. Sakon Masoya
3. Dandalin Soyayya
4. Wasikun Soyayya
5. Dan Soyayya
6. Sarkin Tsari
7. Mallaka
8. Littafin So
9. Birnin Soyayya
A yanzu haka yana da aure da 'ya daya mai suna Ummi. Yana da sha'awar ba da umarni a finafinan Hausa, da sha'awar wasan kwallon kafa. Kuma yana kokarin wucewa karatun digirinsa a kasar waje.

6 comments:

Untitled said...
This comment has been removed by the author.
Untitled said...

Dear Dr. Adamu, I have been following your blog for some time now. Just wondering if you can recommend some Hausa authors? Thanks very much.

albakaye said...

Mallam na ga abnda ka rubuta, ne ma na ye karatu na a Kurna ama 1979 na fara.

I enjoyed reading your story, I also went to Kurna Primary 1979 to 82. Kurna is another world from where I am today. Again thank you and keep writing.

Mubarak said...

Hey Mr. Anka its me Izzah am in Germany, with friends just sarching for Hausa writing thn i meet u on this site am glad to see u on this stage n happy pls my regardz to all Gizo Staff

murtala inuwa said...

Allah yakara maka baiwar rubuce rubucen dakasa agaba daga yayenka Murtala Inuwa daga Sudan

Abdullahi Alhassan said...

Gaskiya saidai san barka idan akayi da la'akarin yadda harkar kasuwancin ka yashara wajen wallafa littafai wanda akowanne yanayi dazamani yazo dashi ba abarka abayaba fatana anan Allah yakara basira Ameen