Wednesday, March 31, 2010

FAUZIYYA D. SULAIMAN


Fauziyya D. Sulaiman wadda aka fi sani da Matar Bello Q far Q an haife ta a unguwar Fagge a Shekarar 1981 ta yi karatuna na Firamare a Makarantar Festival Primary School, daga nan wuce makarantar ‘yammata ta kwana Government Girls Secondary School ‘Yar gaya a shekara ta 1993, bayan ta kammala karatunta na Jiniya ta koma Makarantar Government Girls College Dala ta karasa karatunta daga 1995 zuwa 1998. Daga nan ta yi aure a shekara ta 1999. A shekara ta 2003 ta koma karatu a Makarantar College of Health Sciences, School of Hygiene in da ta yi Diploma a kan Assistant Nutritionist. Daga nan ta yi Certificate a Makarantar School of Management, akan Hotel and Catering Services.

A game da rubutu kuwa ta fara rubuta littafi a shekarar 2002, in da littafi na farko mai suna Me na yi mata?. Daga nan ta ci gaba da rubuta littafi da suka hada da:

Kishin Banza
Guduna Ake yi
Rayuwar ‘Ya Mace
Mece ce Rayuwa
Burin Raina
Karshen Wahala
Labarin Zuciya
Matsalar Mace
Mijin Uwa
Auren Kudi
Duk Abinda Namiji Ya yi


Fauziyya mamba ce a Kungiyar Marubuta ta Najeriya reshen jihar Kano kuma tana rike da mukamin jami’a a majalisar gudanarwa ta Kungiyar tun watan Maris na 2009 har zuwa 2010. Daga nan aka sake zabenta a dai wannan mukami daga watan Maris na 2010 har zuwa watan Maris na 2012 insha Allahu.

8 comments:

KULU BOYI said...

SALAM, DON ALLAH KUSA MUNA LITTAFAN DA SUKE RUBUTAWA BA LABARIN SU KAWAI BA DON MU DA KE ZAUNE ABROAD MU RIKA CIRE KAWAR GIDA.

THANKS MAI SON KARATUN LITTAFAN HAUSA

aliyu dalhatu jama'are said...

har yanzu babu wani sabon rubutu meya faru?

Ammar Suraj said...

ASSLM ALKM
Naa san wasu daga cikin littattafanta, suna da ma'ana matuka gaya. ALLAH YA KARA BASIRA AMIN.

Amira Maharazu Yuguda said...

Dan allah muna son cigaban renanta xanyi da mutum da aljan pls!

Malik al-Ashtar Hamissou said...

Assalamu alaikum,ina yi maku fatan Alkhairi,Allah ya kara maku basira...da Mai kaunar Marubutan Hausa Malik al-Ashtar daga kasar Niger garin Maradi

Unknown said...

Enter your comment...A gaskiya muna godiya ga marubutan hausa Allah ya Kara basira Mai amfani.

Tia Watson said...

I am glad to see this post on your website. It is beneficial for us and can be very useful in our daily life, and we always use your website information and experiences. Anyway, thank you so much.
Seo Services Provider In Delhi

MNB MNB said...

Barka da warhaka da fatan ku wa da kowa ya wuni lafiya