Tuesday, October 7, 2008

NURA ADO GEZAWA


An haifi Nuraddeen Gezawa (SALMAN NHUR) a ranar lahdi shabiyu ga watan janairun shekarar 1980 miladiyya, wadda ta zo daidai da ashirin da hudu ga watan safar na shekarar 1400 hijiriyya. An haife shi ne cikin garin Gezawa na karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano a tarayyar Najeriya. Ya fara karatunsa na muhammadiyya da na boko (firamare da karamar sakandare) a cikin garin na Gezawa, daga shekarar 1986 zuwa 1994. Daga nan sai ya cigaba da karatunsa na babbar sakandare a makarantar kimiyya ta Dawakin Tofa daga shekarar 1994 zuwa 1997. Nuraddeen ya yi aiki da bangaren lafiya na sakatariyar karamar hukumar Gezawa, inda ya koma karatunsa na share fagen shiga Jami'a a C.A.S ta Kano, a shekara ta 2000. Daga nan sai Nuraddeen ya zarce zuwa Jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sokoto a shekara ta 2001. Ko da yake dai hikima ta Ubangiji ta sanya bai samu damar ko da cin karfin karatun a Jami'ar ta Sokoto ba, saboda matsalolin da suka tilasta masa daukar hutun dole.

Nuraddeen ya fara daukar biro ya dora a kan takarda da sunan rubuta littafi a shekarar 1994, kuma littafin farko da ya fara hattama rubutawa shine AN YI TSALLEN... amma littafin da ya fara fitarwa shine RUMBUN TUNANI. Nuraddeen ya yi rubuce-rubucen kirkirarrun labarai da dama, daga cikin su akwai BAKIN RIJIYA wanda ma'aikatar ilimi ta K.E.R.D ta tace a takarda mai taken K.E.R.D/PROP/22/T/V.I/31, tacewar da ta yi sanadiyyar sayen littafin da ma'aikatar ilimi, da ma'aikatar ilimin firamare suka saya.

Kirkirarrun littafan da Nuraddeen ya rubuta sun hadar da;
Rumbun Tunani, Ba Zama, Bakin Rijiya, Laifi Inuwa, Tokar Danasani, An Yi Tsallen, Rai Dangin Goro (Taskata) Gyara Kayanka, Tsaftataccen Mahaukaci, Ba shiga JIrgin Ba, Ramin Kura, da kuma Abu Kamar Wasa.

Haka nan kasancewar Nuraddeen cikakken dan kungiyar ANA reshen jihar Kano, ya gabatar da gajerun labarai a taron ANA da ake yi duk watan duniya, wasu daga ciki sun hadar da; BAKIN DARE, KOWANE GAUTA, UNGULU DA KAN ZABUWA, SAI DA RUWAN CIKI.., SAGAU, GARIN NEMAN GIRA, DA SIRADIN RUBUTU.

Dadin dadawa, Nuraddeen ya yi wakoki da suka hadar da Rubdugu, Kyawun hali, Shugaban Kowa, Kin wanda Ya Rasa da Tarnakin Bakar Rayuwa.

A fagen addinin Musulunci, Nuraddeen ya rubuta littafai kamar haka; Sabani A Duniyar Musulunci da kuma Rudanin Rayuwa Da Musulunci.

Nuraddeen, har ila yau, ya yi rubutun gajerun labaran turanci da suka zama cikin shafuffukan yanar gizon Helium, wadanda suka hadar da My True Colours, The World of Hate, Brave Or Coward?

A halin yanzu Nuraddeen yana daf da komawa don karasa karatun digirinsa na farko. kuma bai yi aure ba ballantana a je ga batun iyali. Babban abin da ya ke burgeshi shine kokarin da aka yi don kyautata rayuwar da tarnakin rayuwa ya cukwikwiye.
Za a iya tuntubar da Nuraddeen Gezawa ta wadannan hanyoyi;
salmannhur@yahoo.com, 07028821493, 08077879218.

1 comment:

Muh'd Faisal Abdulsalam said...

Azahirin gaskiya a duniyar nijeriya musamman bangarannmu arewacin najeriya dakwai tarin masu tsantsar basira wanda zaka kasa bayani saidai kawai kanagani kasan daga Allah ne! Da a tunanina a duniyar marubuta Nazir Adam salih(NAS),Shafiu Dauda Giwa, basu dana'uku! Ashe nakuskuro malam nura lallai nayaba sai yau7/2/011 Allah yabani damar karanta daya daga cikin littattafanka Gyara kayanka lallai nayi matukar mamaki ashe akwai masana kimiyyar daka iya bada gudun mawa a Talifi/Adabi da baduk ma wanda ya karanta Adabin kaiyabayarwaba? Masanin Kimiyya mana! duk wanda yaiya samun zarafin kamalla Kwalejin kimiyya irin na kano musamman dawakin Tofa/kudu lalle ya cancanci wannan suna. Ina fatan Alheri ga reka acikin karatunka dama rayuwarka Allah kuma yakara basira. Daga dan'uwa Muh'd Faisal Abdulsalam,Dawakin-Tofa Science College Class 2010