Wednesday, May 20, 2009

HIRA DA YARON MALAM

Daga Maje El-Hajeej <sirrinsu@yahoo. com>


Nine Bajakaden Abubakar Imam. Cewar Yaron Malam. Tun lokaci da shahararren marubucin da a yau duniyar hausawa ke girmamawa a matsayin kakan marubuta ya amsa kira zuwa ga mahaliccinsa, manazarta suka dukufa domin zurfafa nazarin gano ko wanene zai gaji shi marigayin, tare da rike alkalaminsa ga ci gaba da assasa yanayi da kuma salonsa na imamantar da labari zuwa yadda zai dace da Hausawa da kuma al’adunsu. Musamman ma ko domin dinbim amfanin da a yau littattafansa ke dasu ga dalibai sakamakon sanya su da ake yi a manhajar karatu, da kuma zama tushe da suke yi na fara koyon karatu ga mafi yawancin garuruwan Hausawa.

Duk da dai wannan bakin gumurzu ne, wanda sai an samu sadauki mai akwatin siddabaru, ko kuma yakau dan mayakiya da zasu ja tunga, su kuma yi shahada, sannan su fara fafatawa suyi gumu gami da artabu tamkar a tsibirin Bamuda da yahudu badda musumi. Domin ba aiki ne na mata ba, ballantana gimbiya Assadatu ko Bajakadiya ko kuma Mayakiya suyi hargagagin farawa. Amma Abdullahi Mukhtar da ake yiwa lakabi da Yaron Malam, ya sanya sulke tare da daura damarar karbar wannan garkuwa ta Imam kamar yadda ya bayyanawa wakilinmu Maje El-Hajeej Hotoro.

(An yi wannan tattaunawa da shine a watan Janairun 2007)

Zamu fara da jin tarihinka. Sunana Abdullahi Mukhtar Yaron Malam, an kuma haife ni a 1976 a unguwar Fagge dake karamar hukumar Fagge Kano. Na kuma yi karatun firamare na a Fagge Special daga 1984 zuwa 1988. Inda na karasa karatun firamarena a Gama Sabuwa saboda komawa can da muka yi. Dagan nan kuma ban samu damar ci gaba da karatuna ba, sai aka kaini makarantar allo a garin Hadeja. Wacce ban dade ba aka dawo dani, sakamakon rashin lafiya da na yi, inda na ci gaba da karatun allo. Kafin daga baya na shiga makarantar koyom larabci ta Aliyu Bn Abu Thalib, wacce daga baya aka mayar da ita Umar Bn Khattab dake Gyadi-gyadI a nan Kano daga 1994 zuwa 1999. Lokaci guda kuma ina mai ci gaba da halartar karatun azure. Na sake shiga makarantar koyon larabci ta Rasulul Akram, bayan na kamala na tafi Irshadul Umma Islamic College ta Shahuci da ake kira da Aliya daga 2001 zuwa 2004. Wanda a halin yanzu ina jami’ar Bayero, inda nake karanta aikin jarida. Tare da dan hadawa da kasuwanci.

Shin ko a wacce shekara ka fara rubutu, kuma ko menene ya dauki hankalinka har ka shigo fagen?
Alal hakika zan iya cewa tun farko na taso ne da sha’awar rubuce-rubuce, domin tun ina firamare na kan dauki takarda nayi ta kwafar littafin Baba da Inna da kuma Iliya dan mai karfi a cikin littattafan makaranta na. Sannan kuma ni dama makaranci ne na littattafan labaran Larabci da Hausa. Kamar irinsu Magana Jar ice, Yawon Duniyar Haji Baba, Labaran Da da na Yanzu, da sauransu. Domin ko a lokacin da na ke makarantar Allo, ragowar ’yan uwana almajirai kan zagaye ni na rika basu labarin wani littafi dana karanta. Na fara fitar da littafina na farko ne a 1999 wanda na addini ne mai suna Hukunce-hukuncen Azumi da Addu’o’in Watan Ramadan. Sai kuma Hukunce-hukuncen Jinin Haila, amma ban fitar dashi ba, sai bayan da na fitar da littafina mai suna kissoshin Ahlul Baiti. Dagan an kuma sai na fitar da Bajakade da kuma sirrin aure da ma’aurata, wadanda sune litattafan da suka zama sanadiyyar aka anni a duniyar marubuta.

A halin yanzu ko littattafanka sun kai nawa?
Zuwa yanzu na samu nasarar rubuta littattafai da dama kamar, Bajakade, Mayakiya, Bakin gumurzu, Gimbiya Assadatu, Artabu, Fafatawa, Gumu, Tsiburin Bamuda, Sadauki mai akwatin siddabaru, Tunga, Shahada, Bajakadiya, ‘Yar mai ganye, Yakau dan mayakiya da kuma Yahudu badda Musulmi da kuma na addini da dama.

Ko da wane irin salo kake amfani a rubutunka?.
Salon rubutuna sune salon jarumta, abin dariya, soyayya da kuma hikimar Magana. Jigo kuma shine karfafa akidar addinin musulunci, tsayar da adalci da kuma kyautata zamantakewa tsakanin al’ummar musulmi da kuma wadanda ba musulmi ba.

Mafi yawancin irn wadannan littattafai da suke dauke da abubuwan da ka rubuta akan samu fassarowa ake daga wasu littattafai, shin naka ma fassara ne ko kuma kirkirowa kake yi?
Maganar gaskiya ina kirkirar labari na ne, kuma mafi yawanci duk wanda ya dauko wani littafi ya fassara, sai an samu wasu sun daga sun ce ga daga inda ya fassaro. Amma ni babu wanda zai daga littattafaina yace ga daga inda na fassaro. Sai dai ina karance-karance kamar yadda na fada domin kaifafa basirar da Allah Ya yi min, wanda dama ita baiwa ce, amma ilimi, bincike da kuma tambaya akan abin day a shigewa mutum duhu, sune abincin basira. Sannan juya ilimi daga wani harshen zuwa wani ba laifi bane, matukar anyi hakan ta halattacciyar hanya ba satar fasaha ba.

Ko me zaka iya cewa dangane da kalaman Dakta Malumfashi da kuma na Farfesa Abdallah da suka bayyana cewa nan gaba zaka iya gadar Marigayi Abubakar Imam a fagen rubutu?
Wannan ba a bin mamaki bane idan aka yi la’akari da yanayi da kuma salonsa na ban dariya da dabarun zaman duniya da kuma hikimar Magana. Kana kuma yana gina labarin san e akan sigar zamanin da, sannan wani lokaci yak an jefa soyayya. To idan akayi la’akari da yanayin rubuce-rubucena salon da nake bi kenan. Kumai an matukar samun karfafawa akan wannan salon rubutu nawa, domin farfesa Abdallah yak an kira ni da sabon Abubakar Imam. Sannan musamman ya zaunar dani ya bani labarin dabarun da marigayin ke bi a rubutunsa. Sannan akwai Malam B.K Zariya wanda sunyi zamani da Marigayi Imam, shima takanas yakan kirani ya zaunar dani ya sanar dani tarihin yadda rayuwar Abubakar Imam ta kasance, harma yakan kirani da marigayi Imam.

Shin ko akwai wata kyauta da makarantanka suka taba yi maka wacce ba zaka taba mantawa da ita ba?.
Akwai wata a Bauchi da ta taba yi min kyautar Alqur’ani mai girma, wacce a gaskiya bazan manta da wannan kyautar ba. Sannan kuma masoya daga wurare daban-daban, suna yi min fatan alheri wanda wannan ma babbar kyauta ce, dab a zan manta da ita ba.

Ko a wane irin yanayi ka fi son yin rubutu?
Ina yin rubutu a kowane irin yanayi, amma nafi jin dadin yanayin bayan sallar asuba. Amma a yanzu na dauki wani salo nana yin rubutu a bakin ruwa, ko cikin daji mai bishiyu da kuma ciyayi, ko wajen gari kamar yadda Abubakar Imam ya yi.

Ko shin a matsayinka na dan kasuwa yaya kake hada harkar rubutu da kuma kasuwanci lokaci guda?.
Ai shi rubutu baya hana marubuci yi wasu abubuwan yau da kullum. Misali idan ka dauki marigayi Imam malamin malakaranta ne kuma marubuci lokaci guda. Sannan daga bisani ya zama Editan wata jarida, wanda a wannan lokacin babban aiki ne saboda karancin kayan aiki. Haka ma a yau zaka samu marubuta suna kuma wasu abubuwa na daban, ciki hard a sojoji da ‘yan sanda da sauran ayyukan gwamnati ko kuma na kamfani kuma wannan baya hana su rubutu.

Da kayi maganar kasuwanci sai ka tuno da korafin da wasu marubuta ke yi na matsalar ‘yan kasuwa, wajen rashin sakar musu kudadensu da wuri bayan an sayar da kayansu.?
Lallai kam wannan matsala ce da muka dade muna kuka da ita, amma yanzu alhamduLillahi al’amura sun fara kyautata, domin zaka samu mud a kanmu marubutan muna yabon wasu ‘yan kasuwar da kokarin bayar da kudI akan kari. Su kuma wadanda ake samun jinkirin sun dauki alwashin magance hakan. Sannan kuma kungiyar masu littattafai da kuma ‘yan kasuwa, suna aiki tukuru wajen ganin ta magance wannan matsala. Mu kara hakuri nan ba jimawa ba, komai zai zama tarihi Insha Allahu.

Kwanakin baya kungiyar marubuta ta kasa reshen jihar Kano (ANA) ta jagoranci marubutan Hausa wata tafiya zuwa kasar Nijar. Kasancewar kana cikin shugabannin wannan kungiya, ko wadanne matsaloli da kuma nasarori kuka samu yayin wannan tafiya.?
Makasudin wannan tafiya shine ziyara da kuma taron karawa juna sani tsakanin marubutan Nijeriya da kuma na waccan kasa. Kana kuma da yin bincike akan yanayin zamantakewa da al’adunsu domin samun karin gogewa ga marubutanmu na nan. Matsala kadai da muka samu ita ce ta motarmu da ta lalace, wanda hakan ya tilasta mana yin amfani da guzurinmu domin kara hayar wata motar da ta karasa dam u can. Mun kuma samu nasarori sosai musamman ma na karawa juna sani, sannan ga kuma ziyarar muhimman wurare da muka yi, sun kuma karrama mu sosai domin hidimomi da suka yi man na tsaro da kuma makwanci. Sannan kuma mun fa’idantu matuka gaya , basirarmu ta kara fadada, wanda dama masu hikima sunce tafiya mabudin ilimi.

10 comments:

mohammed said...

SALAM, ALLAH YA KARA TAIMAKAWA YARON MALAM, @Dr.I REALY LIKE YOUR INOVATION AND IAM ALSO ASPIRING TO BE A WRITER, WE NEED PEOPLE LIKE YOU TO GIVE US COURAGE AND GUIDANCE,JAZAKALLAHU BI KHAIRIN..

Mohammad Auwal Sisqou said...

Assalam!
Gaskiya naji dadin wannan hirar, domin na dade ina son sanin tarihin sa da kuma asalin sa sbd burgeni ba yakeyi wajen irin salon labarun sa da iya rubutun sa.
A karshe ina mika ta'aziyar sa ga iyaye da iyalan sa.
Allah ya jikan sa yasa kuma ya huta, in tamu tazo yasa mu cika da kyau da imani.

Unknown said...

Allah Sarki, mu2wa mai yankan kauna, mu2wa mai yanke duk wani buri, na tabbatar da ba dan daukewar da mu2wa ta yi wa yaron Malam ba, da yanzu Allah Kadai Ya san irin gudunmawar da zai bayar wajen cigaban adabin Hausa da ma al'umar Hausan gaba daya, da fatan Allah Ya yi ta lullube shi da rahamarSa, Ya anfanar da shi daga irin kyawawan gudunmawar da ya bayar na yada ilimi ga al'umma, Ya yafe dukkanin kura-kurai da gazawarsa

Abdullahi Ibrahim said...

ALLAH ya jikan rai, Ameen.

Habarugotel said...

Allah sarki, Rayiwa ke nan hakika bazamu manata da gudumowa da "Yaron Malam ya bayaraba, hakika muna alfahri da hakan muna rokon Allah ya kai haske kabarinsa"

Duk da nima almajiri ne, amma ina sha'awar karance - karance tsahon lokaci muna bibiyar abunda suka wallafa, Allah yayiwa marubatanmu albarka ya hade kawunan su.

DENAWATRICK TECH LTD said...

ALHAMDULILLAH MUNGODE ALLAH YA JIKANKA YA KUMA MAKA RAHAMA.

Unknown said...

Allah ya gafarta masa

Unknown said...

Allah yajikan yaron malam marubucin littafin yahudu badda musulmi

Anonymous said...

Allah ya jikanka da rahana yaron mallam

Anonymous said...

Allah yaji kan yaron malam yayi mishi Rahama