Monday, October 19, 2009

TA'AZIYYAR HADI ABDULLAHI ALKANCI



Hagu zuwa dama: Danjuma Katsina, Hadi Alkanci, Yusuf Adamu a wani taro a Kano


Allah ya yi wa Marubuci Hadi Abdullahi Alkanci rasuwa ranar Litinin 12 ga Oktoba 2009 a Sakkwato bayan ya sha fama da rashin lafiya. Rasuwar Alkanci babban rashi ne ga marubuta da manazarta da ma al'umar Nijeriya. Allah ya jikansa da gafara ya kuma albarkaci bayansa.
Bayan sanarwar da na yi a dandalin marubuta kamar haka:

Salam,Ina bakin cikin sanar da ýan uwa cewa Allah ya yi wa Hadi Abdullahi Alkanci rasuwa jya da yamma a Sakkwato, ya yi fama da rashin lafiya wajen watannin uku, mun yi rashi babba, muna kuma rokon Allah ya gafarta masa ya kuma jikansa da rahma amin. Muna rokon yan uwa su yi masa addu'a koyaushe, ga dan takaitaccen tarihinsa nan a wannan rariyar likau
http:// marubutanhau sa.blogspot. com/2008/ 09/hadi-abdullah i-alkanci. html

Allah ya gafarta masa ya kuma sa mu ma mu cika da imani amin. Dr Yusuf Adamu

Mun samu sakwannin taáziyya da dama, ga kalilan daga cikinsu a kasa:

Ado Ahmad Gidan Dabino
ALLAH AKBAR, Allah ya ji kan Hadi Abdullahi Alkanci. Marubucin Soyayya Ta Fi Kudi (littafin wasan kwaikwayo) da Harsashin Kasa da Shin So Gaskiya Ne? da sauran su. Babu shakka mun yi babban rashi a fagen marubuta, haziki gwarzo a fagen fasaha ya tafi.

Ba zan manta da haduwa ta ta karshe da Hadi ba a lokacin da ya zo Kano wajen bikin kaddamar da littattafan Bashir Othman Tofa, yana cikin mutanen hudu da na yi hira da su a ciki shirin da nake gabatarwa a gidan rediyo FREEDOM mai suna Alkalami Ya Fi Takobi, mutane sun yaba da ire-iren bayanan da ya yi sosai, kuma in yana magana lallai ka san cikakken mutumin Sokoto ne, mai iya karin magana da dabarun zance.Lokacin da na ji labarin rasuwarsa ta hanyar SMS daga Yusuf Adamu ina jihar Lagos, ba shakka na kadu sosai da ganin wannan sakon.

ALLAHU AKBAR! ALLAHU !! AKBAR!!! Allah ka rahamshe shi, ka sa ya huta, mu kuma Allah ya kyauta tamu in ta zo. Allah ka sa gidan Aljanna ce makomarmu baki daya. Amin!!! Ina mika sakon gaisuwa ga dukkanin 'yan'uwa da abokan arziki da dukkan Sakkwatawa.


***
JAMILU NAFSENCIBIYAR LAFAZIN HAUSA
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI' UN....Aduk sa'ilin da muka ji wannan kalma tuni take mana nuni da wani gagarumin abu ne ya auku.hakanne yasa nima ina samun wannan rashin jangwarzo mai bada gudunmawa musamman aharkar wasanni, abunda na iya furtawa kenan tare da tawassali da cewa muma tamu tananan zuwa. sai dai muce ubangiji ya kai rahma agareshi. mu kuma Allah yasa mu cika da imani, amin.

*****
Mamane Sahabi Ousmane Alias M.SONiamey Niger
Allahu akbar haka ne, Allah yaji kanshikuma ya sa, ya huta.abida ya bari Allah yabasu hakurida masoya da kuma yan uwa. mu kuma da muka rage in tamu ta zoAllah ya sa, mugama da iskan duniya lafiya Amin.ita rayuwa haka take, kowa lokacin shi, zai jira.ba'a gaggauta wa kowa, kuma ba'a jinkirta wa kowa. kulli nafsi za'ikatil mautko wace rai! sai ta dan-dana mutuwa.gaba dayan mu, muci gaba da yi wa junan mu, addu'a.intamu ta zo, Allah ya sa mucika da kalmar La'ilaha illallah Muhammadu Rasulullah.

******

Sarkin yan Nijar,
Atta Oumaten
إنا لله وانا اليه راجعون منهـا خلقناكم وفيهـا وعيدكم ومنهـا نخرجكم تارةاخرى
Dawannan nake meka tsakon ta'aziyar daukacin yan Nijar dake cikin wadannan zauruka, ga iyalai da abokan arziki na wannan ba wan Allah, allah yasa ya huta mu kuma idan tamu tazo Allah yasa mucika da imani.
***
Uba Dan Zainab
Allah yayimasa rahama yasada shi da annabi sallalahu alaihi wasallamzuriyarsa kuma Allah yashiga lamuransu yasakasu bin surad'al mustaqeem.

****
Ahmad Yahuza Getso (B.A. MIAD, MPPA, HPDCS)
Allah ya gafarta masa ya kyautata tamu.
***
Muhammad Muhammad
Allah ya gafarta masa, mu kuma Allah ya kyauta karshen mu.
***
Isa Muhammad Inuwa
Allah Ya jikan Babban Marubuci Hadi Alkanci, Ya sa mutuwa hutu, Ya kyauta namu zuwan, Ya sa mu je a sa'a. Amin!

****
Muhammad Mansoor
Allah ya sa ya huta amin suma amin.
****
Ibrahim Sheme
Allah Ya jikanshi, ya yi masa rahama. Allahu Akbar! One of the last Titans of Classic Hausa Literature. Wallahi mun yi rashi.
****
Bala Muhammad (A Daidaita Sahu)
Innalillahi Wa inna Ilaihir Raji'un. Allah ya jikansa ya gafarta masa. In tamu ta zo Allah ya sa mu cika da imani, amin.

****
Aisha Zakari
Allah ya jikansa ya gafarta masa, lallai kam mun yi babban rashi.
****
Dr Wale Okediran (ANA President)
May his soul rest in perfect peace, amin.
***
Danjuma Katsina
A gaskiya mun yi rashi babba, Allah ka jikan wannan bawa naka ka gafarta masa amin.
***
Alhaji Kabiru Katsina
Allah ya gafarta masa, mun yi rashin jagora a rubutu.
***
Dr. Aliya Adamu
Allah ya Jikansa ya gafarta masa amin.

NASIRU G AHMAD YANAWAKI

An haifi Nasiru G. Ahamd a unguwar ‘Yan Awaki cikin Birnin Kano, ran 6 ga Safar, 1384, BH. (4/2/1964). Bayan karatun Alkur’ani, ya yi makarantar Firamare Islamiyya ta ‘Yan Awaki, daga 1975-1981. Ya wuce zuwa makarantar Nazarin Addinin Musulunci mai zurfi ta Shahuci (1981-1985). Sai Makarantar Nazarin Shari’ar Musulunci ta Aminu Kano, (1986-1989) inda ya samu diploma a Harsunan Hausa da Larabci da Nazarin Addinin Musulunci. Daga (1993-1996), ya je Jami’ar Usmanu Dan Fodiyo ta Sakkwato, inda ya samu digirin farko a harshen Hausa.
A shekarar 1984, ya halarci ajin koyon buga keken rubutu (Typewriting) da ke karkashin Hukumar Yada Ilimin Manya ta Kano, a 1992, ya halarci wani kwas da Jami’ar Musulunci ta Madina ke shiryawa, don horar da malaman Arabiyya da addinin Musulunci, a Jami’ar Bayero ta Kano. A 1992 din dai, ya je wani kwas na addinin Musulunci, a garin Idah, cikin jihar Kogi. A 1999, ya yi wani kwas na karatun gida, karkashin “Sincere Writers Club”, inda ya samu takardar shaida (certificate) kan aikin jarida.
A 1991, ya je jihar “Cross Rivers” inda ya yi aikin jami’i mai duba Malaman Kidaya (Supervisor). Ya koyi sarrafa na’ura mai kwakwalwa a aikace, (Practical) a “Urgent Computers” inda ya taba yin aiki. Yana cikin masu duba wakar Hausa, ta jarrabawar ‘W.A.E.C.’ Wakili ne na jaridar “People And Events”. Editan littattafai ne mai zaman kansa. Ya yi aikin koyarwa a makarantu da dama, (Firamare da Sakandare) tun daga 1984 zuwa yanzu. Yana da sha’awar ziyarce-ziyarce da kulla abota, da karance-karance a kowane fannin ilimi da rayuwa. Ya rubuta litattafai da dama, da wakoki jingim. Nasiru kuma na cikin Sahún gaba na ‎ ‘yan Kungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA) reshen jira Kano. A halin yanzu yana karatun digirinsa na biyu a Jamiár Ahmadu Bello (ABU) Zaria.

Monday, June 22, 2009

MUHAMMAD USMAN


Muhammad Usman wanda kuma aka sani da Sunusi Shehu Daneji na daya daga cikin turakun da su assassan adabin Hausa na zamani. Marubuci, mai dab'i kuma mai wallafa mujallar Hausa. Marubuci ne wanda ya ci gaba da bada jagora ga marubutan Hausa na zamani tare da kokarin samar da adabi mai tarbiyya. Yana rubuce-rubuce na tarbiyya da kimiyyar sararin samaniya da sauransu. Cikin litattafansa akwai:

Bankwana da Masoyi

Yaron Kirki

Madubin Imani

HAFSATU AHMAD ABDULWAHID


An haifi Hajiya Hafsatu a Birnin Kano. Ta yi karatunta na boko a Kano kafin ta yi aure ta koma Gusau da zama. Fitacciyar marubuciyar Hausa ce wadda littafinta na So Aljannar Duniya shi ne littafin zube na farko da mace ta rubuta a harshen Hausa. Ta wallafa 'Yardubu Mai Tambotsai da kuma Saba Dan Sababi. Tana kuma rubutu da turanci da kuma fillanci. Marubuciya ce wadda ke da kishin rubutu ta kan kuma halarci tarurrukan marubutan Hausa da na Nijeriya. Bayan rubutu takan taba siyasa don ta taba takarar Gwamna a jihar Zamfara.

Sunday, June 14, 2009

BASHIR OTHMAN TOFA



Fitaccen dan siyasa kuma hamshakin dan kasuwa wanda kuma ya yanke shawarar yin amfani da basirar da Allah ya yi masa ya zama marubuci. Bashir Tofa ya yi rubuce-rubuce da harshen Hausa bisa zabin ciyar da harshen gaba. Ya wallafa litattafan Hausa da dama wadanda suka hada da na kirkira da kuma na ilmi. Cikin litattafansa da suka fito sun hada da:

Amarzadan a Birnin Aljanu
Amarzadan da Zoben Farsiyas
Kimiyyar Sararin Samaniya
Tunaninka Kamanninka
Kimiyya da Al'ajaban Al-Qur'ani
Gajerun Labarai
Mu Sha Dariya
Rayuwa Bayan Mutuwa

Saturday, June 13, 2009

BINTA RABIÚ SIPIKIN



(Za mu kawo bayanai a kanta bada jimawa ba)

UMMA SULAIMAN 'YAN AWAKI


Fitacciyar marubuciyar Hausa Umma Sulaiman 'Yan Awaki... (za mu kawo bayanan nan gaba kadan)

UMMA ADAMU


An haifi Umma Adamu ranar 15th ga Oktoba 1981 a Gwarzo, duk da cewa ita 'yar asalin Hadejia ce. Ta yi karatun Firamare a Kanti Primary School Kazaure daga 1987-2003. Ta kuma yi karatun

Sakandare a Malam Madori da Sakandaren Kimiyya ta Taura inda ta gama a 1999. Ta ci gaba da karatu daga 2000 a School of Health Technology Jahun da Informatics Institute Kazaure da kuma Jigawa State College of Education har zuwa 2006. A halin yanzu (2009) tana karatu ne a Kano State University of Science and Technology Wudil. Cikin litattafan da ta buga sun hada da:

1. Raino, 2. Rigakafi 3. Sirrinus ko Sirrimu 4. Wahayi 5. Zaman Jira 6. Ya Zalince ni 7. Sabanin Ra'ayi 8. Abu a Duhu.

Tana sha'awar koyarwa da kallon fina-finai da tafiye-tafiye da koyarwa da kuma rubuta kirkirarrun labaru.

Wednesday, May 20, 2009

HIRA DA YARON MALAM

Daga Maje El-Hajeej <sirrinsu@yahoo. com>


Nine Bajakaden Abubakar Imam. Cewar Yaron Malam. Tun lokaci da shahararren marubucin da a yau duniyar hausawa ke girmamawa a matsayin kakan marubuta ya amsa kira zuwa ga mahaliccinsa, manazarta suka dukufa domin zurfafa nazarin gano ko wanene zai gaji shi marigayin, tare da rike alkalaminsa ga ci gaba da assasa yanayi da kuma salonsa na imamantar da labari zuwa yadda zai dace da Hausawa da kuma al’adunsu. Musamman ma ko domin dinbim amfanin da a yau littattafansa ke dasu ga dalibai sakamakon sanya su da ake yi a manhajar karatu, da kuma zama tushe da suke yi na fara koyon karatu ga mafi yawancin garuruwan Hausawa.

Duk da dai wannan bakin gumurzu ne, wanda sai an samu sadauki mai akwatin siddabaru, ko kuma yakau dan mayakiya da zasu ja tunga, su kuma yi shahada, sannan su fara fafatawa suyi gumu gami da artabu tamkar a tsibirin Bamuda da yahudu badda musumi. Domin ba aiki ne na mata ba, ballantana gimbiya Assadatu ko Bajakadiya ko kuma Mayakiya suyi hargagagin farawa. Amma Abdullahi Mukhtar da ake yiwa lakabi da Yaron Malam, ya sanya sulke tare da daura damarar karbar wannan garkuwa ta Imam kamar yadda ya bayyanawa wakilinmu Maje El-Hajeej Hotoro.

(An yi wannan tattaunawa da shine a watan Janairun 2007)

Zamu fara da jin tarihinka. Sunana Abdullahi Mukhtar Yaron Malam, an kuma haife ni a 1976 a unguwar Fagge dake karamar hukumar Fagge Kano. Na kuma yi karatun firamare na a Fagge Special daga 1984 zuwa 1988. Inda na karasa karatun firamarena a Gama Sabuwa saboda komawa can da muka yi. Dagan nan kuma ban samu damar ci gaba da karatuna ba, sai aka kaini makarantar allo a garin Hadeja. Wacce ban dade ba aka dawo dani, sakamakon rashin lafiya da na yi, inda na ci gaba da karatun allo. Kafin daga baya na shiga makarantar koyom larabci ta Aliyu Bn Abu Thalib, wacce daga baya aka mayar da ita Umar Bn Khattab dake Gyadi-gyadI a nan Kano daga 1994 zuwa 1999. Lokaci guda kuma ina mai ci gaba da halartar karatun azure. Na sake shiga makarantar koyon larabci ta Rasulul Akram, bayan na kamala na tafi Irshadul Umma Islamic College ta Shahuci da ake kira da Aliya daga 2001 zuwa 2004. Wanda a halin yanzu ina jami’ar Bayero, inda nake karanta aikin jarida. Tare da dan hadawa da kasuwanci.

Shin ko a wacce shekara ka fara rubutu, kuma ko menene ya dauki hankalinka har ka shigo fagen?
Alal hakika zan iya cewa tun farko na taso ne da sha’awar rubuce-rubuce, domin tun ina firamare na kan dauki takarda nayi ta kwafar littafin Baba da Inna da kuma Iliya dan mai karfi a cikin littattafan makaranta na. Sannan kuma ni dama makaranci ne na littattafan labaran Larabci da Hausa. Kamar irinsu Magana Jar ice, Yawon Duniyar Haji Baba, Labaran Da da na Yanzu, da sauransu. Domin ko a lokacin da na ke makarantar Allo, ragowar ’yan uwana almajirai kan zagaye ni na rika basu labarin wani littafi dana karanta. Na fara fitar da littafina na farko ne a 1999 wanda na addini ne mai suna Hukunce-hukuncen Azumi da Addu’o’in Watan Ramadan. Sai kuma Hukunce-hukuncen Jinin Haila, amma ban fitar dashi ba, sai bayan da na fitar da littafina mai suna kissoshin Ahlul Baiti. Dagan an kuma sai na fitar da Bajakade da kuma sirrin aure da ma’aurata, wadanda sune litattafan da suka zama sanadiyyar aka anni a duniyar marubuta.

A halin yanzu ko littattafanka sun kai nawa?
Zuwa yanzu na samu nasarar rubuta littattafai da dama kamar, Bajakade, Mayakiya, Bakin gumurzu, Gimbiya Assadatu, Artabu, Fafatawa, Gumu, Tsiburin Bamuda, Sadauki mai akwatin siddabaru, Tunga, Shahada, Bajakadiya, ‘Yar mai ganye, Yakau dan mayakiya da kuma Yahudu badda Musulmi da kuma na addini da dama.

Ko da wane irin salo kake amfani a rubutunka?.
Salon rubutuna sune salon jarumta, abin dariya, soyayya da kuma hikimar Magana. Jigo kuma shine karfafa akidar addinin musulunci, tsayar da adalci da kuma kyautata zamantakewa tsakanin al’ummar musulmi da kuma wadanda ba musulmi ba.

Mafi yawancin irn wadannan littattafai da suke dauke da abubuwan da ka rubuta akan samu fassarowa ake daga wasu littattafai, shin naka ma fassara ne ko kuma kirkirowa kake yi?
Maganar gaskiya ina kirkirar labari na ne, kuma mafi yawanci duk wanda ya dauko wani littafi ya fassara, sai an samu wasu sun daga sun ce ga daga inda ya fassaro. Amma ni babu wanda zai daga littattafaina yace ga daga inda na fassaro. Sai dai ina karance-karance kamar yadda na fada domin kaifafa basirar da Allah Ya yi min, wanda dama ita baiwa ce, amma ilimi, bincike da kuma tambaya akan abin day a shigewa mutum duhu, sune abincin basira. Sannan juya ilimi daga wani harshen zuwa wani ba laifi bane, matukar anyi hakan ta halattacciyar hanya ba satar fasaha ba.

Ko me zaka iya cewa dangane da kalaman Dakta Malumfashi da kuma na Farfesa Abdallah da suka bayyana cewa nan gaba zaka iya gadar Marigayi Abubakar Imam a fagen rubutu?
Wannan ba a bin mamaki bane idan aka yi la’akari da yanayi da kuma salonsa na ban dariya da dabarun zaman duniya da kuma hikimar Magana. Kana kuma yana gina labarin san e akan sigar zamanin da, sannan wani lokaci yak an jefa soyayya. To idan akayi la’akari da yanayin rubuce-rubucena salon da nake bi kenan. Kumai an matukar samun karfafawa akan wannan salon rubutu nawa, domin farfesa Abdallah yak an kira ni da sabon Abubakar Imam. Sannan musamman ya zaunar dani ya bani labarin dabarun da marigayin ke bi a rubutunsa. Sannan akwai Malam B.K Zariya wanda sunyi zamani da Marigayi Imam, shima takanas yakan kirani ya zaunar dani ya sanar dani tarihin yadda rayuwar Abubakar Imam ta kasance, harma yakan kirani da marigayi Imam.

Shin ko akwai wata kyauta da makarantanka suka taba yi maka wacce ba zaka taba mantawa da ita ba?.
Akwai wata a Bauchi da ta taba yi min kyautar Alqur’ani mai girma, wacce a gaskiya bazan manta da wannan kyautar ba. Sannan kuma masoya daga wurare daban-daban, suna yi min fatan alheri wanda wannan ma babbar kyauta ce, dab a zan manta da ita ba.

Ko a wane irin yanayi ka fi son yin rubutu?
Ina yin rubutu a kowane irin yanayi, amma nafi jin dadin yanayin bayan sallar asuba. Amma a yanzu na dauki wani salo nana yin rubutu a bakin ruwa, ko cikin daji mai bishiyu da kuma ciyayi, ko wajen gari kamar yadda Abubakar Imam ya yi.

Ko shin a matsayinka na dan kasuwa yaya kake hada harkar rubutu da kuma kasuwanci lokaci guda?.
Ai shi rubutu baya hana marubuci yi wasu abubuwan yau da kullum. Misali idan ka dauki marigayi Imam malamin malakaranta ne kuma marubuci lokaci guda. Sannan daga bisani ya zama Editan wata jarida, wanda a wannan lokacin babban aiki ne saboda karancin kayan aiki. Haka ma a yau zaka samu marubuta suna kuma wasu abubuwa na daban, ciki hard a sojoji da ‘yan sanda da sauran ayyukan gwamnati ko kuma na kamfani kuma wannan baya hana su rubutu.

Da kayi maganar kasuwanci sai ka tuno da korafin da wasu marubuta ke yi na matsalar ‘yan kasuwa, wajen rashin sakar musu kudadensu da wuri bayan an sayar da kayansu.?
Lallai kam wannan matsala ce da muka dade muna kuka da ita, amma yanzu alhamduLillahi al’amura sun fara kyautata, domin zaka samu mud a kanmu marubutan muna yabon wasu ‘yan kasuwar da kokarin bayar da kudI akan kari. Su kuma wadanda ake samun jinkirin sun dauki alwashin magance hakan. Sannan kuma kungiyar masu littattafai da kuma ‘yan kasuwa, suna aiki tukuru wajen ganin ta magance wannan matsala. Mu kara hakuri nan ba jimawa ba, komai zai zama tarihi Insha Allahu.

Kwanakin baya kungiyar marubuta ta kasa reshen jihar Kano (ANA) ta jagoranci marubutan Hausa wata tafiya zuwa kasar Nijar. Kasancewar kana cikin shugabannin wannan kungiya, ko wadanne matsaloli da kuma nasarori kuka samu yayin wannan tafiya.?
Makasudin wannan tafiya shine ziyara da kuma taron karawa juna sani tsakanin marubutan Nijeriya da kuma na waccan kasa. Kana kuma da yin bincike akan yanayin zamantakewa da al’adunsu domin samun karin gogewa ga marubutanmu na nan. Matsala kadai da muka samu ita ce ta motarmu da ta lalace, wanda hakan ya tilasta mana yin amfani da guzurinmu domin kara hayar wata motar da ta karasa dam u can. Mun kuma samu nasarori sosai musamman ma na karawa juna sani, sannan ga kuma ziyarar muhimman wurare da muka yi, sun kuma karrama mu sosai domin hidimomi da suka yi man na tsaro da kuma makwanci. Sannan kuma mun fa’idantu matuka gaya , basirarmu ta kara fadada, wanda dama masu hikima sunce tafiya mabudin ilimi.

TA'AZIYYAR YARON MALAM

Allah ya yi wa Abdullahi Muktar Yaron Malam rasuwa ranar Lahadi 17 ga Mayu 2009 da misalin sha biyu na rana, a dakin Karatu na Muratala Muhammad dake birnin Kano. Ya rasu ya bar mata daya da diya uku. Fitaccen marubuci, shugaban Brigade Authors Forum (BAF) kuma jami'i a Kungiyar Marubuta ta Nigeria (ANA) reshen Jihar Kano, Yaron Malam marubuci ne ingarma wanda ya bada muhimmiyar gudunmuwa wurin ci gaban adabin Hausa. Yaron Malam kuma mawallafi ne kuma mai sayar da littattafai. Mun yi babban rashi. Allah ya jikan Yaron Malam ya gafarta masa amin.


Dr Yusuf M Adamu
Shugaban ANA Kano

Dannan wannan rariyar likau don karanta takaitaccen tarihin Abdullahi Muktar Yaron Malam: http://marubutanhausa.blogspot.com/2009/02/abdullahi-mukhtar-yaron-malam.html

Saturday, May 2, 2009

KABIRU YUSUF ANKA



An haifi Kabiru Yusuf Fagge (anka), a unguwar Fagge. Ya fara karatun Alkur'ani a makarantun allo, da Islamiyya ta Sabilul Rashad da ke Gyadi-gyadi da Mukhtariyya Islamiyya da ke unguwar Fagge da kuma Thimarul Kur'an (bangaren dare) ya sami saukar Kur'ani, da karanta sauran littattafan addini.
Ya fara karatun Firamare a Kurna Special Primary School da sakandire a JSS Kurna,  Sai Jami'ar Bayero inda ya sami shaidar Diploma a bangaren aikin jarida (Mass Communication), sannan kuma ya samu shaidar karatun Diploma a bangaren Statistics, da kuma Diploma a na'ura mai kwakwalwa (Computer) a makarantun: Online Computer da kuma Hands-On Computer Institute inda ya karanci (Desktop Publishing da Data Processing and Maintenance), ya karanci Diploma in Film and Television Production a Northwest University, Kano, a wannan shekara ta 2020 yana Jami'ar Bayero, yana karantar Hausa.
Ya sami kwarewa a fannin sarrafa na'ura mai kwakwalwa musamman a bangaren zane da bugu (design graphics and typing).
Ya buga littattafai, jaridu da mujallu masu yawa a bugun kwamfiyuta, ya kuma tsara shafukan mujallu da jaridu da kuma tsara bangwayen littattafai da yawa.
Ya yi rubuce-rubuce a jaridu da mujallu  kamar haka:-
Wakiliya -(mujallar Marubuta) - a matsayin mataimakin Edita.
Inuwar Marubuta -(mujallar Marubuta) - marubuci na musamman
Suda -(mujallar 'yan fim) - marubuci
Kwallon Kafa -(mujallar labarun wasanni) -mataimakin Edita.
Muryar 'Yanci -(jaridar labaran karamar hukumar Fagge) -Edita
Masoya -(mujallar labaran rayuwa da soyayya) - Edita
Kakaki -(mujallar kare ra'ayin karamar hukumar Fagge) -Edita
Haka ya yi rubuce-rubuce da dama a jaridu da mujallu na kasar nan. Ya wallafa littattafai da dama.

YADDA YA SAMI KANSA A RUBUCE-RUBUCE
Tun a aji hudu na firamare ya zama mai iya karance-karancen littattafan Hausa da Jaridu, shi da wani abokin karatu mai suna Abdulhamid Muhammad Al'ansari wanda asalinsa Kwara ne, da shi suke siyo littattafan da jaridu suna karantawa, don haka sai ya fara karanta MAGANA JARI CE a ajinsu, daga nan ya sami kan sa a rubuce-rubuce.
LITTAFAN DA YA RUBUTA
Ya rubuta littattafai da dama, amma wadanda ya fitar guda goma bangaren hikaya:
1. Karfin Hali
2. Shure-shure
3. Ninkaya
4. Alwashi
5. Bilkisu
6. Firgita Samari...
7. Rayya
8. 'Yanmata
9. Kushewar Badi
10. Launin So

Sai kuma littattafan ilimi na koyarwa
The Boy Who Cried Wolf (anthology of short stories)
Dabarun Rubuta Kagaggun Labarai
Mu Koyi Karatu 1,2,3,4,5
Tatsuniyoyi Da Labarun Gargajiya

Sai kuma littafan WASAN KWAIKWAYO:
1. KOWA YA YI DA KYAU
2. TUTAR BABU
3. KURMAN AMO

Sai kuma littattafan da suka shafi bandariya da sauran hikaya
1. Mu Sha Dariya
2. Kai Ma Ka Dara
3. Abokin Dariya
4. Malamin Ban Dariya
5. A Ba Su Dariya
6. Gidan Dariya
7. Zunbuli Kakan Marowata

Sannan akwai littattafan da suka shafi koyar da yara kanana karatu da rubutu kamar:
1. Standard Dictionary
2. The Boy Who Cried Wolf
3. Alphabet for Kids
4. Mathematics for Kids
5. Successful Drawing Book for Children
Da sauransu

FINA-FINAI
Ninkaya, 
Sulusi, 
Sakin Aure, 
Hakkin Miji, 
Aure Ibada Ne, 
Sallamar Bankwana, 
Sharri Kayan Kwalba, 
Karshenki, 
Matar Waye?, 
Mahaifiyarmu, 
Wa Ya Kasheta?, 
Dan Garba, 
Sarkin Barayi, 
Sarkin Aska, 
Kwalba
Wace Ce Ni?
Goyon Kaka

Series
'Ya'yanmu, 
Mu Sha Dariya, 
Butulcin Zuci


Yana da aure da 'ya'ya

Sunday, February 22, 2009

ABDULLAHI MUKHTAR (YARON MALAM)


An haife shi ranar 1/6/76 a unguwar Fagge. Ya yi makarantar Fagge Special Primary School Ibrahim Taiwo Road. Daga nan suka koma Birged da zama inda ya karasa firamare a Birged Special primary School. Ya shiga Aliyu Bn Abu Talib School daga 1991-1996. Daga nan ya koma makarantar zaure don ci gaba da karatun addini zuwa 2005. A 2005 ne ya yi karatun Professional Diploma a BUK.
Litattafansa na Hausa sun hada da:
Bajakade
Mayakiya
Bakin Gumurzu
Gimbiya Assadatu
Artabu
Gumu
Tunga
Bajakadiya'(Ýar Mai ganye)
Sihirtacciya
Yahudu Badda Musulmi
Tsibirin Bamuda
Yakau
Sirrin Aure da Maáurata A Muslunci
Duniyar Maáurata A Muslunci
Ku Tambayeni Kafin Ku Rasa Ni
Kuriá
Hukunce-Hukuncen Jinin Haila
Hassada da Maganinta A Muslunci
Kissoshin Ahlul Baiti

Friday, February 20, 2009

ZAHARADDEEN IBRAHIM KALLAH


Zaharaddeen Ibrahim Kallah ya yi digirinsa a kan ilimin zamantakewar dan Adam da kuma siyasa. Marubuci ne da yake rubutu a harsuna guda biyu, hausa da turanci. Ya taba lashe gasar rubutun waka ta turanci ta duniya a shekara ta 2004, da Negerian.Biz suka shirya. Yana daga cikin shugabanni gudanarwa na ANA. A hali yanzu yana aiki da Strategic Planning a Jami’ar Bayero ta Kano. Ya rubuta littafin Karkon Dabino sannan ya fito a littafai na gamayya da suka hada da Five hundred Nigerian poets, da Mazan Fara. Littafansa da suke hanyar fitowa sun hada da So ko Wahala da Usman Mai duniya da Lokaci Bako ne da Love in Mayuwandu tare da The Right Choice.