Friday, December 5, 2008

AISHA ZAKARI




Aisha Zakari 'yar asalin Hadejia, fitacciyar marubuciya ce, kodayake ta fi karfi a rubutun turanci daga baya ta fara rubutun Hausa. Ta samu digirinta na farko a fanning Labarin Kasa (Geography) daga Jamiár Bayero ta Kano kuma tana cikin wadanda suka rubuta wani wasan kwaikwayo na gidan Radiyon BBC watau Gatanan Gatananku ta kuma rubuta waken turanci da dama wadanda aka buga a litattafai da kuma gidajen yana. Ta taba zama Magatakardar Kudi ta Kungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA) ta Kasa kuma ta rike mukamai a ANA Kano da dama hard a na Mataimakiyar Shugaba. Aisha Fellow ce ta Leadership Development Mechanism (LDM Fellow) kuma tana daya daga cikin hazikan matasa da suka taimakawa adabin Hausawa da Hausawa kuma a halin yanzu tana zaune da mijinta a Amurka inda take ci gaba da karatu.
Littafinta da ta rubuta ko ta fito a ciki sun hada da:
Himma Ba Ta Ga Raggo
Verses in Absentia Poetry of Aisha Usman Bugaje (Coeditor)
Pregnant Skies: Anthology of 50 Nigerian Poets
Mazan Fara: ANA Zamfara Anthology of Poems and Short Stories

Tuesday, October 7, 2008

NURA ADO GEZAWA


An haifi Nuraddeen Gezawa (SALMAN NHUR) a ranar lahdi shabiyu ga watan janairun shekarar 1980 miladiyya, wadda ta zo daidai da ashirin da hudu ga watan safar na shekarar 1400 hijiriyya. An haife shi ne cikin garin Gezawa na karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano a tarayyar Najeriya. Ya fara karatunsa na muhammadiyya da na boko (firamare da karamar sakandare) a cikin garin na Gezawa, daga shekarar 1986 zuwa 1994. Daga nan sai ya cigaba da karatunsa na babbar sakandare a makarantar kimiyya ta Dawakin Tofa daga shekarar 1994 zuwa 1997. Nuraddeen ya yi aiki da bangaren lafiya na sakatariyar karamar hukumar Gezawa, inda ya koma karatunsa na share fagen shiga Jami'a a C.A.S ta Kano, a shekara ta 2000. Daga nan sai Nuraddeen ya zarce zuwa Jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sokoto a shekara ta 2001. Ko da yake dai hikima ta Ubangiji ta sanya bai samu damar ko da cin karfin karatun a Jami'ar ta Sokoto ba, saboda matsalolin da suka tilasta masa daukar hutun dole.

Nuraddeen ya fara daukar biro ya dora a kan takarda da sunan rubuta littafi a shekarar 1994, kuma littafin farko da ya fara hattama rubutawa shine AN YI TSALLEN... amma littafin da ya fara fitarwa shine RUMBUN TUNANI. Nuraddeen ya yi rubuce-rubucen kirkirarrun labarai da dama, daga cikin su akwai BAKIN RIJIYA wanda ma'aikatar ilimi ta K.E.R.D ta tace a takarda mai taken K.E.R.D/PROP/22/T/V.I/31, tacewar da ta yi sanadiyyar sayen littafin da ma'aikatar ilimi, da ma'aikatar ilimin firamare suka saya.

Kirkirarrun littafan da Nuraddeen ya rubuta sun hadar da;
Rumbun Tunani, Ba Zama, Bakin Rijiya, Laifi Inuwa, Tokar Danasani, An Yi Tsallen, Rai Dangin Goro (Taskata) Gyara Kayanka, Tsaftataccen Mahaukaci, Ba shiga JIrgin Ba, Ramin Kura, da kuma Abu Kamar Wasa.

Haka nan kasancewar Nuraddeen cikakken dan kungiyar ANA reshen jihar Kano, ya gabatar da gajerun labarai a taron ANA da ake yi duk watan duniya, wasu daga ciki sun hadar da; BAKIN DARE, KOWANE GAUTA, UNGULU DA KAN ZABUWA, SAI DA RUWAN CIKI.., SAGAU, GARIN NEMAN GIRA, DA SIRADIN RUBUTU.

Dadin dadawa, Nuraddeen ya yi wakoki da suka hadar da Rubdugu, Kyawun hali, Shugaban Kowa, Kin wanda Ya Rasa da Tarnakin Bakar Rayuwa.

A fagen addinin Musulunci, Nuraddeen ya rubuta littafai kamar haka; Sabani A Duniyar Musulunci da kuma Rudanin Rayuwa Da Musulunci.

Nuraddeen, har ila yau, ya yi rubutun gajerun labaran turanci da suka zama cikin shafuffukan yanar gizon Helium, wadanda suka hadar da My True Colours, The World of Hate, Brave Or Coward?

A halin yanzu Nuraddeen yana daf da komawa don karasa karatun digirinsa na farko. kuma bai yi aure ba ballantana a je ga batun iyali. Babban abin da ya ke burgeshi shine kokarin da aka yi don kyautata rayuwar da tarnakin rayuwa ya cukwikwiye.
Za a iya tuntubar da Nuraddeen Gezawa ta wadannan hanyoyi;
salmannhur@yahoo.com, 07028821493, 08077879218.

Sunday, September 28, 2008

BARKA DA SALLAH

Da fatan kowa ya yi sallah lafiya. Allah ya ba mu ladan azumi ya kuma maimaita mana mu ga ta badin badadadadada... amin summa amin.

ZAKARIYA MUHAMMAD SARKI


An haifi Zakariyya Muhammad Sarki, a garin Kazaure ta Jihar Jigawa a shekarar 1976. Bayan karatun Muhammadiya, ya yi karatun Firamare da na karamar Sikandire a Kudu Central Primary da kuma Sikandiren Gwamnati da ke Kazaure a in da ya kamala a shekarar 1991. A lokacin ne kuma sha’awar rubuce-rubuce da karance-karance musamman na marubuta hausawa ya fara shiga zuciyarsa. Wannan ya sa ya zama mafi iya karatun littafi a cikin yan’uwansa dalibai. Duk da dai ba zai iya tuna labari daya da ya taba rubutawa ba a wancan lokaci, ya ‘saukewa’ yan ajinsu na firamare da na sikandire littatafai na Hausa irin su Magana Jari Ce, Iliya Dan Maikarfi, Da’u Fataken Dare, Dare Daya da dai sauran irin su sau bila adadin.Ya kamala karatun Sikandirensa a Sikandiren kimiyya ta gwamnati da ke Kafin Hausa a Jihar Jigawa a shekarar 1994. Ya samu shiga Makarantar Nazarin Addinin Musulunci da Shari’a ta Malam Aminu Kano (Legal), a nan ya samu shedar Diploma a kan Shari’a (Law) a shekarar 2003. Daganan ya wuce zuwa Jami’ar Bayero da ke Kano in da ya samu shedar samun Digiri na farko a fannin ilimin halayya da zamantakewar al’umma, (Sociology).. A yanzu haka kuma yana kan fara karatun Digirinsa na biyu a sabon zangon Karatu mai zuwa (2008/2009) a Jami’ar Bayero da ke Kano.

Zakariyya ya taba aikin kamfani a Kano da Legas a tsakanin shekarun 1995 zuwa 1999. Aikin da ya yi a Legas ya ba shi damar yin rubuce-rubuce a wasu fitattun jaridu na Kudancin Nijeriya kamar ‘The Punch’, ‘The Post Express’ da dai sauran irinsu. Haka kuma Zakariyya ya taba zama babban wakili (Bureau Chief) na Legas na kamfanin jaridar ‘The Shield Weekly’ da kuma Garkuwa da ke Kano. Ya taba zama wakilin Mujallar Fim a Kano. Hakanan kuma Marubuci na Musamman ga tsohuwar Mujallar ‘Mumtaz’ ta shahararren marubucin nan Ado Ahmad Gidan Dabino.

Zakariyya ya rubuta littattafai da kuma wakoki kirkirarru masu dama sai dai kuma ba’a taba buga ko daya daga ciki ba saboda wani shiri da yake da shi nan gaba (a shekarar 2009). Duk da haka a shekarar 2005 an juya littafinsa mai suna “Wuta a Masaka” zuwa fim mai taken “Wahami”, wanda darakta Ado Gidan Dabino ya bada Umarni. Zakariyya memba ne na Kungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA) reshen Jihar Kano. Ya na da mata da ya’ya biyu, kuma yanzu yana zaune a Kano.

Za a iya ziyartar blog din shi mai adireshi kamar haka http://www.zakariyyasarki.blogspot.com/
Ko kuma adireshin email : zakariyyasarki2005@yahoo.co.uk, zakariyyasarki@ymail.com
Lambobin Waya : 080-24388438, 064-893104, 064-317582.
** Mun buga wannan marubuci duk da cewa bai taba fidda littafi ba, bisa dalilai biyu, na farko dai mu kara masa kwarin gwiwa na biyu kuma tinda suna cikin na farko da suka turo ya samu wannan loto.

Thursday, September 11, 2008

BASHIR YAHUZA MALUMFASHI


An haifi Bashir Yahuza Malumfashi a ranar 15 ga watan Mayu na shekarar 1967 a garin Malumfashi, Jihar Katsina. Ya yi karatun firamare a Tunau Primary School, Unguwar Sodangi, Malumfashi, daga 1973 zuwa 1980. Daga nan ya wuce zuwa Government Day Secondary School, Malumfashi, daga 1981 zuwa 1986. Ya samu zuwa Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a (CAS, Zaria), daga shekarar 1987 zuwa 1989. Bai ci gaba da karatu ba saboda matsalar rashin lafiya da ta same shi, amma daga bisani ya shiga Kwalejin Horar da Jami'an 'Yan Sanda ta Kaduna (Police College, Kaduna), inda ya samu horo kan aikin 'yan sanda. Ya yi karatun Diploma a fannin Hikimar Koyar da Turanci (Diploma in Language Education, English) a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina. Haka kuma ya yi karatun Diploma kan ilimin sarrafa kalmomi (Diploma in Computer Data Processing) a wata makarantar Kwamfuta mai zaman kanta. Ya halarci kwasa-kwasai da tarukan kara wa juna ilimi a fannoni da dama. Ya fara aikin 'yan sanda ne a garin Dutsin-ma, Jihar Katsina, inda daga nan ya koma Kurfi, duk dai a Jihar Katsina. Daga bisani aka sake yi masa canjin wurin aiki zuwa Funtua, duk dai a Jihar Katsina. Ya samu canjin wurin aiki daga Funtua, aka mayar da ni zuwa Katsina. Daga nan ne aka mayar da shi aiki zuwa Abuja, inda na yi aiki a Babban Ofishin Binciken Laifuffuka na Hukumar 'Yan Sanda ta Kasa (Force Criminal Investigation Department), Area 10, Abuja. Mafi yawan aikinsa na 'yan sanda, ya yi shi ne a bangaren binciken laifuffuka da neman labarin sirri. A shekarar 2005 ne ya yi ritaya daga aikin 'yan sanda, bayan ya shafe shekaru 17 a kan aiki ke nan.

Ta bangaren harkar rubuce-rubuce kuwa, dama can shi mai sha'awar karance-karance da rubuce-rubuce ne. Ya fara rubutu tun yana aji uku a sakandare (1983), inda ya rubuta littafina na farko wanda ba a buga ba har yanzu. Sunan littafin Bak'i Da Fari, amma an karanta shi a Gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna, a filinsu na Shafa Labari Shuni. Daga nan ya ci gaba da rubuce-rubuce, ana bugawa a jaridun Hausa da na Turanci, musamman ma Gaskiya Ta Fi Kwabo, Nasiha, Almizan, Katsina News Week, New Nigerian, Weekly Trust, da sauransu. Littafinsa na farko da aka buga kuma ya fito kasuwa shi ne Babban Tarko, wanda ya fito a cikin shekarar 1997. Sai kuma na biyu mai suna Bak'in Kishi, wanda ya fito kasuwa a shekarar 2003. Yakan rubuta wakoki na Hausa da na Turanci, wadanda ake yawan bugawa a jaridu. Littafina da ke kan hanyar fitowa, shi ne Zinatu Matar Gwamna, wanda aka dade ana tsakura shi a cikin jaridar Aminiya.

A tarihin rubuce-rubuce, ya shiga gasar rubutu da dama, inda a shekarar 1995 da 1996 na samu kyaututtuka daga gidan rediyon Muryar Nijeriya, Lagos, a sakamakon zuwa na biyu da mukalolina suka a yi a shekarun na jere. A 2004 ma ya samu nasarar zuwa na daya a gasar rubuta labarai da gidan rediyon BBC suka sanya, mai taken Labarina.

Bayan ya yi ritaya daga aiki 'yan sanda a shekarar 2005, sai ya fada aikin jarida, inda ya ci gaba da aiki da Mujallar Fim, wacce dama na dade yana aika masu rubuce-rubuce tun daga fitowarta. Ya rike mukamin Manajan Edita na mujallar, inda ya zauna Kano. Daga baya ya koma Kaduna, inda ya fara aiki da jaridar Turanci mai suna Public Agenda, a matsayin Editan Shafukan Adabi. A cikin shekarar 2006 ne ya bar wannan jarida, ya koma aiki a kamfanin Media Trust Limited, masu wallafa jaridun Daily Trust, Weekly Trust, Sunday Trust da kuma Aminiya. A jaridar Aminiya nake, inda shi ne Editan Shafukan Adabi da Nishadi na jaridar, duk da cewa yakan taimaka da rahotanni ga sauran jaridun Turanci na kamfanin, daga lokaci zuwa lokaci.
A halin yanzu, yana da aure da 'ya'yaye. Babban burinsa a duniya shi ne, na son ya ga harshen Hausa ya bunkasa, ya zama babba a duniya; kamar kuma yadda yake son ganin cewa ya zama babban marubuci, don ba da gudunmowata ga al'umma.

Littattafansa na Hausa da suka fito sune:

1- Babban Tarko - 1997.
2- Bakin Kishi - 2003

http://us.f431.mail.yahoo.com/ym/Compose?To=byahuza03@yahoo.com
GSM: 08020968758, 08065576011.

Tuesday, September 9, 2008

MUHAMMAD LAWAL BARISTA

Muhammad Lawal Barista, Sakataren Kungiyar Inuwar Marubuta watau HAF sanannen marubuci ne kuma dan jarida wanda a halin yanzu yana karatu a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya na J amiár Bayero ta Kano. Mamba ne kuma na ANA Kano. Litattafansa na Hausa da aka buga sune:
Sakon Mutuwa
Makahon So
Buduri
Bakin Kishi
A Dalilin Talla…
TA Cuce Ni
Karshen So
Matan Zamani
Kasafi

SA'ADATU BABA AHMAD



Sa’adatau Baba Ahmad wadda makaranta suke fi sani da Ýar babanta na daya daga cikin fitattun marubuta mata na zamani. A halin yanzu tana karatun digiri na farko a jamiár Bayero ta Kano kuma jamiá ce a Kungiyar ANA Kano da kuma Hausa Authors Forum (HAF). Jerin litattafanta na Hausa da suke fito sune:

Wahala Siradin Rayuwa 1, 2
Yi Wa kai 1,2
Taka Tsantsan da Maza 1,2
Baram-Baram 1,2,3
Kishiya Ba Laifi Ba Ce 1,2,3
Rabon Bawa da Arziki
Mu Kame Kanmu
Auren Yanzu 1,2
Ban Karya Alkawari Ba 1,2,3
Zawaran Zamani 1,2,3
Kaddara ko Kishi 1,2
Birni da Kauye 1,2
Kantafi
Hasken Rana 1,2,3
Sirrin Zuciyata 1,2
Mutuwar Tsaye
Sallamar Bankwana
Zuciyar Kauna
Duhun Dare
Gudun Talauci

Monday, September 8, 2008

MAWALLAFA WAKOKIN HAUSA

Wannan jerin sunaye na marubutan wake na Hausa na dauko shi ne daga cikin mashahurin litattafin nan na Marigayi Ibrahim Yaro Yahaya ne watau HAUSA A RUBUCE. Allah ya jikan Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya amin.


Marubuta daga yankin Sakkwato

1. Wazirin Gwandu Alhaji Umaru Nasarawa
2. A Maikudu Gidadawa
3. M. Abubakar Maikaturu
4. Alkali Alhaji Bello Gidadawa
5. Alhaji Shehu Shagari
6. Alkali A. Umaru Alkanci
7. Malam Bello Alkanci
8. Malam Mahe Hubbare
9. Alhaji Yusufu Kantu
10. Alhaji Sambo Wali
11. Malam Khalilu Marinar Tsamiya
12. Malam Maharazu Kwasare
13. Alhaji Sa’adu Usman Zuru
14. Sarkin Baura Umaru
15. Alhaji Garba Gwandu
16. Alhaji Mazuga
17. Alhaji Audu Gwandu
18. Alhaji Muhammad Mahe Kambarawa
19. Alhaji Alhaji Dogon Daji
20. Alhaji Umaru Birnin Kebbi
21. Alhaji (Dr) Waziri Junaidu
22. M Buharin Liman an Wuri
23. M. Muhammad Tambari Kubuda
24. M Abdulkadir Gidan Sa’i
25. Alkali Halliru Wurno
26. M Muhammad Dan Baddo Gwandu
27. Alhaji Mustafa Sabon Birni
28. Malam Usman Dan Goggo
29. Mallam Adamu Koko
30. Mallam Mande Abubakar B/kebbi
31. Mallam Audu Makaho
32. Mallam Umaru Gandu
33. Mallam Shehu Saraki
34. Alhaji Abubakar Koko
35 Alhaji Abdulrazak Yaldu


Marubuta daga yankin Kano
36. Malam Mu’azu Hadeja
37. Malam Shehu Nasiru Kabara
38. Alhaji Mudi Sipikin
39. Malam Aminu Kano
40. Alhaji Akilu Aliyu
41. Malam Liman Dan Amu
42. Malam Muhammadu Namaigangi Danbatta
43. Malam Ya’u Sitti
45. Alhaji Tijjani Tukur Yola
46. Alhaji Sunusi Danbaba
47. Alhaji Yusufu Abdullahi Bichi
48. Alhaji Baba Mai Gyada
49. Alhaji Na’ibi Sulaimanu Wali
50. Dr. Isa Hashim
51. Alhaji Yunusa Dayyabu Ibrahim
52. Alhaji Abdullahi Makarantar Lungu
53. Alhaji Ibrahim Yaro Muhammad
54. Alhaji Lawan Mai Turare
55. Mallam Balarabe Kurawa
56. Mallam Hamisu Yadudu
57. Mallam Muhammadu Na sani Umai
58. Mallam Muhammadu Bashir Sai’du Yan Tandu
59. Abubakar Dangani Bakin Ruwa
60. A.Ibrahim Tijjani Dukawa
61. A.Aminu Babangida Yalwa
62. Mallam Muhammadu Zaiyanu
63. Ali Usudu Tudun Makera
64. Malam Wada Hamza
65. Alhaji Rabiu Ahmadu Na Shehu
66. Alhaji Ahmadu Tireda Kabawa
67. Mallam Muhammad Dan Jinjiri Mai Adu’a
68. Alhaji Shehu Mu’azu Galadiman Kano
69. Alhaji Adamu Na Ma’aji
70. Alhaji Yusufu Adamu Galadanchi
71. Alhaji Auwalu Sheshi
72. Alhaji Sani Farisa
73. Alhaji Bala Yandoya
74. Ahaji Amadi Yaro
75. Alhaji Nasiru Jikan Sarkin Agadasawa
76. A.Muhammadu Sadisu Sagagi
77. A.Adamu Jingau
78. A.Adamu Sandalo Sudawa
79. A Kabiru Inuwa Magoga
80. Hajiya Hauwa Gwaram
81. Hajiya Rukayyatu Sabuwa
82. A.Hassan Babaru Lollokin Lemo
83. A.Ibrahim Katala
84. A.Ahmadu Danmatawalle
85. A. Sharifi Tijjani
86. A.Sule B/K Zaria
87. A.Sagir Usman B/Ruwa
88. M.Aminuddeen Abubakar
89. Alhaji Aliyu Abdulkadir Zango


Marubuta daga yankin Zaria
89. Sarkin Zazzau Alu Dan Sidi
90. Alhaji (Dr.) Aliyu Namangi
91. Alhaji (Dr.) Abubakar Imam
92. Alhaji Abubakar Ladan
93. M Muhammad Balarabe Umar
94. M. Garba Likoro
95. Malam Lawan na Cediyar Karauka Mai Ra’iyya
96. A. Talle Yahaya
97. M Garban Garba Zaria
98. M. Sarki Aliyu Dini
99. A Ladan Na Sharaihu
100. M. Almu Layin T/Wada Zaria
101. M Yahaya Dikko

Marubuta daga yankin Katsina
102. A. Audu Sandada
103. A. Shehu Mai Gidaje
104. A Muhammadu Anda Na Garba ABCD
105. A. Hassan Nagogo
106. A. Muhammmadu Sani Jari Dangani
107. A. Muhammadu Makari

Marubuta daga yankin Bauchi
108. M. Sa’adu Zungur
109. Limamin Bauchi A Ahmadu
110. Shehu Malam Dahiru Usman
111. A. Hassan Kosasshe112. A. Dahiru Musa Jahun Bauchi

Marubuta daga yankin Kaduna
113. A Abubakar Mahmadu Gumi
114. A. Hassan Idris Kusada
115. A. Abdullahi Zakari Kwara
116. A. Garba ABCD

Marubuta daga yankin Jos
117. A. Gambo Hawaja
118. A. Lawan Taura
119. A. Inuwa Alin Iliya

Marubuta daga sauran wurare
120. A. Shehu Adamu Kontagora
121. A. Salihu Kontagora
122. A. Garba Jikan Hinde Gashuwa
123. M. Mamuda Akilu Aliyu Nguru
124. A. Hamidu Zailani Yola
125. A. Danlami Limamin Agege
126. A. garba Affa Azare
127. A. Aminu Balarabe Gusau

Ina godiya ga Muhammad Yusuf da Hauwa Hassan Ismaíl wadanda suka taimaka wurin sake juyar mun wadannan sunaye.

BALARABA RAMAT YAKUBU


An haifi Balaraba Ramat Yakubu a Birnin Kano a shekarar 1958. Bayan neman ilminta na Islamiyya da na Boko daga shekarar 1962 zuwa 1980, Balaraba Ramat ta tsunduma wurin rubuce-rubuce masu koyar da zaman duniya da tunatarwa ga jamaá. A halin yanzu ita ce shugaba daraktar gudanarwa ta kamfanin Ramat General Enterprises da Mukaddas Nigeria Limited da kuma Ramat Productions Limited. Ta rike mukamai a kungiyoyin marubuta da dama, it ace mataimakiyar shugabar Raina Kama Writers Association, ta taba rike mukamin ma’aji a Kungiyar Marubuta ta Nijeriya reshen Jihar Kano (ANA Kano). A halin yanzu it ace shugabar Kallabi Writers Association. A halin yanzu tana da ýaýa biyar da jikoki uku, kuma ta rubuta litattafai har guda tara. Hajiya Balaraba ta samu kyaututtuka akan rubuce-rubucenta kamar kyautar taron Marubuta na Arewacin Nieriya da kuma kyautar adabi ta Engineer Kazaure. Bayan wannan masana na gida da wajen Nijeriya sun yi nazarce-nazarce da dama akan rubuce rubucenta. Kuma ta yi fice a Littattafanta sun hada da:

Budurwar Zuciya (1987)
Wa Zai Auri Jahila (1990)
Alhaki Kwikuyo
Badariyya
Wane Kare ne ba bare ba?
Matar Uba Jaraba
Ilmin Gishirin Zamani
Ina Sonsa Haka
Kyakkyawar Rayuwa

HADI ABDULLAHI ALKANCI


Fitaccen marubucin Wasan Kwaikwayo na Hausa Hadi Abdullahi Alkanci, an haife shi ranar 1 ga janairu 1957 at Alkanci, Birnin Sakkwato. Ya yi karatu a Kofar Marke Nizzamiyya school (yanzu ana cewa makarantar Alhaji Alhaji Model Primary School, Sokoto). A shekarar 1973 ya tafi Sultan Abubakar College Sokoto, inda y agama da Grade II Teacher a 1977. Ya yi aiki a sashen Ilmi na Karamar Hukumar Sakkwato, ya koyar a Army Children School Sokoto daga 1977-78. Daga nan ya tafi Staff Training Centre (yanzu College of Administration, Sokoto) inda ya yi satifiket kan Fassaradaga 1978-79. Ya yi aiki a Rima Radio Sokoto daga nan ya yi ritaya ya fara kasuwanci, a wannan lokaci ya tan tabawa N.T.A Lagos, aiki inda yak e gabatar da wani shiri mai suna "WAZOBIA" ya kuma dan taba aikin karatun labarum duniya duk daga 1981-82. Ya zama daya daga cikin manyan daraktocin ALKANCI ENTERPRISE. A wannan lokaci ya samu damar ziyartar kasashen duniya da dama. A shekarar 1986 ne ya bar harkar kasuwanci ya dawo ya dukufa wurin harkar rubutu da aikin jarida. Malam hadi Alkanci ya gabatar da makalu iri daban daban a tarurruka na marubuta da adabi a jamióí daban da ban na kasar nan kuma fitaccen marubucin wasan kwaikwayo ne na Hausa. A shekarar 1981 ne aka buga littafinsa na farko mai suna Soyayya Ta Fi Kudi wanda sashen aládu na Maáikatar Aládu ta tarayya ta buga. Ya rubuta littattafai da dama wasu daga cikinsu sun hada da:
Soyayya Ta Fi Kudi (Wasan Kwaikwayo)
Harsashin Kasa
Karatun A cikkin Hotona 1
Shin So Gaskiya Ne?
Zaben Allah
Jagora Ga Mai Aikin Hajji
Bayansu akwai litattafai da dama day a rubuta wadanda ba a buga ba. Mamba ne na ANA Sokoto. Malam Hadi ya bada gdunmuwa sosai wurin habaka adabin Hausa musamman a Sakkwato kuma duk wanda ya sanshi a sakkwato a yau to a marubuci ya san shi. A halin yanzu shi n eke buga mujallar Sahihiya a Sakkwato.

Sunday, September 7, 2008

Sakwannin Ba da Kwarin Gwiwa

Wadannan sakwanni ne na ba da kwarin gwiwa da na fara samu daga marubuta da makaranta. Na ji dadinsu kuna ina fatan wannan ya zama alama ta irin goyon bayan da wannan aiki zai samu. Ba aika na ne ni kadai ba, aikinmu ne gaba daya kuma muna rokon kowa ya ba da gudunmuwarsa.

“Salam, Madalla da wannan gagarimin aiki naka,Allah ya saka da alheri amadadin marubuta,duk da dai mu 'yan kallo ne amma abin yayi dai dai.da fatan za'a sha ruwa lafiya amin
Daga Sunusi Bature Dawakin Tofa,Freedom (FM) Kano

“Tare da sallama. Malam barka da wannan gagarumin kokari, sai dai mu ce (marubuta) Allah ya saka da alkairi. Tambaya daya ce, shin ba za a iya shiga cikin dandalin kai tsaye ba, a aika da sakon? Kuma shafin ya tsaya ne a iya tarihin marubuta, ko kuma akwai wasu bayanai na al'amuran yau da kullum da suka shafe.Da fatan an sha ruwa lafiya, Allah ya ba mu lada da falolin da ke cikin wannan wata mai alfarma, amin summa amin.,
Daga Kabir Anka

"Wannan ba karamin kokari ka yi ba don adana tarihi da hotunan mutane masu basira da fasaha a waje daya yadda masu bincike za su sami sauken tattara bayanan da suke nema game da marubutan ba. Allah ya yi jagora, amin”.
Daga Ado Ahmad Gidan Dabino

“Assalamu Alaikum, Ranka Ya Dade!!! Barka da wannan babban kokari, hakika wannan aiki ne wanda ya kasance abin yabawa da kuma jinjinawa a gareka, domin samun irin ka a cikin al’umma ba su da yawa. Ka kawo wani babban ci gaba wanda ba a taba samun irin sa ba, sannan kuma ka kawo hanyar da duk duniya zata san Marubutan Adabi da kuma littattafan Adabi wanda a da sai wane da wane ne suke samun damar sanin su. Wannan wata hanya ce wacce su kansu Marubutan Adabi za su dage dantse wajen ganin sun inganta aikinsu kasancewar wannan wata babbar allura ce wacce ta fi ta sojoji sa kaimi da zagewa, tun da a halin yanzu duk duniya ce ta ke kallon su.

“A karshe kuma ina ganin ya kamata a rika hadawa da email din Marubuci, don wasu basu da blog wanda za a samu bayaninsu a ciki. Bayan haka, idan da hali ina ga ya kamata duk littafin da aka sa sunan sa to a bude masa shafi yadda idan har mai bincike yana bukatar karantawa zai iya karantawa ta cikin wannan fage. Jinjina mai yawa da wannan babban Jihadi, Allah Ya biya ka da gidan Aljannah. Da fatan Allah Ya sa ‘yan baya mu yi koyi!!!”

Daga Mohd Mohd Assadiq


“Masha Allah...muna nan tafe...Allah ya bar girma, mu ci gaba da samu daga fasaha da ilimunku.... A sha ruwa lafiya.”
Daga Umar Mannoter

Salam a gaskiya wannan abu ne da ya zama abin alfahari gare mu hausawa da ma harshen hausa, wannan na nuna mana cewa zuwa wani lokaci za a kara samun ci gaba a wannan harshe namu na hausa.mun godeDAG IBRAHIM YARO D/TOFA MEDIA TRUST LIMITED ABUJA[JARIDAR AMINYA]

AUWALU YUSUFU HAMZA










An haifi Auwalu Yusufu Hamza a 1959 a Nguru Jihar Yobe, kodayake, iyayensa mutanen Utai ne cikin Karamar Hukumar Wudil, Jihar Kano. Ya yi karatunsa a Jamiár New York, Amurka inda ya yi digiri a fanning Nazarin Al’adu (Anthropology). Bayan ya dawo Nijeriya ya fara aiki a History and Culture Bureau ta Jihar Kano inda ya yi jagorar kafa ANA reshen jihar Kano. Ya bar History and Culture Bureau a 1997. Daga baya ya yi aiki a CRD watau Center for Research da Documentation Kano da kuma SLPG Dutse Jihar Jigawa. Shine jamiín da ya dage wajen tabbatar da cewa an samu reshen ANA a Kano lokaci yana aiki a HCB, kokarinsa ne ya jawo aka fara kafa ANA Kano a 1992, wadda ba ta je koína ba ta rushe, da aka sake kokarin sake kafa ta a 1995, ya bada gudunmuwa babba daga nan kuma ANA Kano ta ci gaba da wanzuwa har yau. Ya taba zama Shugaban ANA Kano daga 1998-2000. Saboda tsarin ayyukansa ya samu zagayawa kauyukan arewancin arewar Nijeriya kuma rubuce-rubucensa na nuni da yadda rayuwa take a kauyukan kasar Hausa. Yana rubutu da Hausa da kuma Turanci.




Litattafansa na Hausa sune:
Gidan Haya
‘Yarkwatano

Littattafansa na Turanci sune:
Love Path
A Question of Marriage
Open Courts
Citizens Parade

ADO AHMAD GIDAN DABINO



An haifi Ado Ahmad Gidan Dabino a Danbagina Karamar Hukumar Dawakin Kudu a shekarar 1964, ya yi karatun allo a Zangon Barebari. Bai samu damar yin karatun boko ba sai da ya kai shekara ashirin, sannan ya fara zuwa makarantar yaki da jahilci ta masallachi, watau makarantar da aka fi sani a Kano da makarantar Baban Ladi,daga nan ya yi karatun Sakandare a GSS Warure inda ya samu SSCE a 1990. Daga nan ya yi kwas na shekara guda akan karatun makafi da koyon aikin kafinta, A shekarar 2005 kuma ya sami diploma akan aikin sadarwa daga jamiár Bayero ta Kano. Ado Ahmad na daya daga cikin fitattun marubutan Hausa na zamani kuma littafinsa mai suna In da So da Kauna na daya daga cikin fitattun littattafan Hausa na kowane zamani. Ya rike mukamai da dama a Kungiyoyin marubuta, shi ne shugaban Kungiya Marubuta ta Raina Kama, ya taba zama Mataimakin shugabna ANA reshen Kano, ya zamar mata maáji kafin ya zama shugabanta tun 2006 zuwa yau. Ya taba zama Edita na FIM magazine kasancewar daya daga cikin wadanda suka kafata a 1999. Shi ne mawallafin Mumtaz kuma shugaba/daraktan gudanawarwa na Gidan Dabino International Nigeria Limited. Ya gabatar da makalu a manyan tarrurruka na karawa juna sani a jami'oí daban daban na Nijeriya. Dan wasan Hausa ne, dan jarida kuma mawallafi. Litattatafansa da suka fito sune:

In Da So da Kauna 1 da 2 (1991)
Hattara Dai Masoya 1 & 2, (1993)
Masoyan Zamani 1& 2, (1993)
Wani Hani Ga Allah 1 & 2, (1995)
Duniya Sai Sannu (1996)
Kaico (1997)
Sarkin Ban Kano (2004) tare da Sani Yusuf Ayagi

An fassara wasu dag cikin litattafansa kamar haka:

The Soul of My Heart (Translation of In Da so Da Kauna), (1994)
Nemesis (Translation of Masoyan Zamani) 1996

Ana iya samun Karin bayani game da rubuce-rubucensa a http://www.gidandabino.blogspot.com/
Email address: gidandabino@yahoo.com

Friday, September 5, 2008

YUSUF M. ADAMU


Yusuf Muhammad Adamu wanda yanzu aka fi sani da Yusuf Adamu na daya daga cikin fitattun marubutan Hausa na zamani. An haife shi a Katsina a shekarar 1968. Ya yi karatun firamare a Giginyu Primary School Kano daga 1974-1980. Ya tafi Sakandaren Gwamnati ta Koko cikin Jihar Kebbi daga 1980-1983 daga nan ya wuce Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati dake Zuru jihar Kebbi daga 1983-1985. A nan ne, ya fara rubuta littafinsa na farko watau Maza Gumbar Dutse. Ya samu shiga jamiár Usmanu Danfodiyo Sakkwato daga 1985-1990 inda ya samu digirinsa na farko a fanning Labarin Kasa (BSc Geography). A Jami’ar sakkwato ya rike mukamin Babban Magatarka na Kungiyar Hausa kuma Wazirin Sarkin Hausawa. Ya yi hidimar kasa (NYSC) a Dutsin Ma, inda ya koyar da Geography a Government Science Secondary School Dutsin Ma. A 1994 kuma ya samu digirinsa na biyu daga Jami’ar Ibadan. Ya fara aiki a Jamiár bayero ta Kano a 1995. A shekara ta 2004 kuma ya samu digirinsa na uku watau PhD a Geography. Yak ware ne a fanning Medical Geography. Yana da shaáwar gudanar da nazarce-nazarce akan lafiyar mata, kiwon lafiya, adabin Hausa na zamani da kuma fadadar birane.

Dk. Yusuf Adamu ya rike mukamai da dama a Kungiyoyin Marubuta. Ya taba zama shugaban Kungiyar Matasa Marubuta, ya kuma rike mukamin Magatakarda a Kungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA) reshen jihar Kano daga 1995-2000. Daga 2000-2006 ya zama Shugaban ANA Kano. Ya kuma taba zaman dan majalisar gudanawar na ANA ta kasa daga 1997-2001. Yana rubutu a harshen Hausa da kuma Turanci.

Litattafansa na Hausa na kirkira da aka buga sune:

Idan So Cuta Ne (1989)
Ummul-khairi (1995)
Maza Gumbar Dutse (2007)

Sauran litttafansa na Hausa (na kirkira) da ya gama amma ba a buga ba sun hada da:

Dukan Ruwa (1988)
Son Zuciya Bacinta (1989) Wasan Kwaikwayo
Gumakan Zamani (1992)
Zainab (yana kan aiki a kansa)

Littattafansa na Turanci kuma wadanda aka buga sune:
Butterfly and other poems (1995)
My first book of rhymes (1998)
Litters (2000)
Pregnant Skies: Anthology of 50 Nigerian poets (2003)
Landscapes of Reality (2007)
Animals in the Neighbourhood (2007)
Mazan Fara: ANA Zamfara Anthology (2008)
Kwaryar Kira (ANA Kano Hausa Anthology) tare da Ado Ahmad Gidan Dabino (2010)

Litattafan Ilmi da ya tace (co-editor)

Inequality in Nigeria: A Multidisciplinary Perspective (2003) tare da M.B. Shitu

Hausa Home Videos: Technology, Economy and Society (2003) tare da A.U. Adamu da U.F. Jibril

Corporate Survival, Competitiveness and Consumer Satisfaction in Nigerian Industries (2005) tare da M.S. Sagagi
Readings in Social Science Research (2006) tare da Habu Muhammed da K.I. Dandago

Introduction to Social Sciences (2008) tare da M.A. Yusuf da A.A. Adepoju

Email addresses: yusufadamu2000@yahoo.com /yusufadamu@gmail.com

JERIN SUNAYEN MARUBUTA HAUSA (MATA)

Wannnan jerin sunayen marubutan Hausa ne mata. Shi ma wannan somin tabi ne, muna fatan mu ci gaba da sa sunayen sauran marubuta. Duk wanda ya ga cewa a kwai sunan marubuciyar da ba a saba don Allah ya tuntube mu. Mun gode kwarai.


Aishah Abdulhameed
Aisha Zakari
amina Hassan Abdullahi
Balaraba Ramat Yakubu
Bilkisu Baban Dede
Bilkisu Funtua
Bilkisu Yusuf Ali
Fatima Sulaiman Gunya
Fauziyya Danladi Sulaiman
Habiba Imam Ikara
Hadiza Alfa Mohd
Hadiza Abdullahi
Hadiza Nuhu Gudaji
Hadiza Salisu Sharif
Hadiza Sani Garba
Hafsatu Ahmad Abdulwahid
Halima Yusif Ali
Hauwa Hassan
Jamila Abdullahi R/Lemo
Kilima Abba Siri-siri
Lubaba Ya'u
maimuna I.Y. Yahaya
Maryam Ali Ali
Maryam Kabir Mashi
Nafisa Muda Lawal
Rabiá tu Fagge
Rabi Talle Maifata
Rabi Yusuf Yakasai
Rahama Majid
Saádatu Baba Ahmad
Saliha Abdullahi
Talatu Wada Ahmed
Sadiya Garba Yakasai
Umma Sulaiman Ýan Awaki
Umma Aliyu Musa
Zainab Auwal
Zainab Kabir Biroman
Zuwaira Isa

JERIN SUNAYEN MARUBUTAN HAUSA (MAZA)

Wannan jeri ne na marubutan Hausa maza. Jerin ya hada da marubuta na da da na yanzu, kuma ya hada da masu rubutun zube da na wasan kwaikwayo da wake. Wannan jeri bai hada kowa da kowa ba, za mu ci gaba da inganta shi lokaci zuwa lokaci. In wani ya ga cewa akwai marubucin da ya sani ba a sa shi ba to ya tuntube mu. Mun gode kwarai.



Abdulkadir Dangambo
Abdullahi Muktar Yaron malam
Abubakar Imam
Abubakar Tafawa Balewa
Abubakar Tunau Mafara
Adamu Muhammed
Ado Ahmad Gidan Dabino
Ahamd Muhammad Zaharaddeen
Ahmadu Ingawa
Ahmed Sabir
Akilu Aliyu
Ali Aliyu Abubakar
Aminu Hassan Yakasai
Aminu Salisu
Aminuddeen Ladan Abubakar (ALA)
Auwalu Yusufu Hamza
Bala Anas Babinlata
Balarabe Yakasai
Bashari Farouk Roukbah
Bashir Sanda Gusau
Bashir Yahuza Malumfashi
Bature Gagare
Dan Azumi Baba C/Ýan Gurasa
Danjuma Katsina
Hadi Abdullahi Alkanci
Haidara Aliyu
Hamisu Bature
Ibrahim Hamza Abdullahi Bichi
Ibrahim Malumfashi
Ibrahim Sheme
Ibrahim Yaro Muhammad
Ibrahim Yaro Yahaya
Idris S Imam
Iliyasu Umar (Maikudi)
Kabir Assada
Kabiru Sulaiman Yakasai
Kabiru Yusuf Ankah
Kubra Abdullahi
Magaji Dambatta
Magaji Lawan Shitu
Maigari Ahmed Bichi
Maje El-Hajeej
Malam Aminu Kano
Muázu Hadejia
Mudi Sipikin
Muhammad Lawan Barista
Muhammad Usman
Munir Mamman
Nasiru G Ahmed ‘Yan Awaki
Nazir Adam Salih
Nura Ahmad
Nura Azara
Saádu Zungur
Sadi Mandawari
Salihu Kontagora
Salisu Maiunguwa D/Iya
Sulaiman Ibrahim Katsina
Umaru Dembo
Umaru Isa Galadanchi
Yushaú Muhammed
Yusuf Lawan Gwazaye
Yusuf M Adamu
Yusuf Shehu
Zaharaddeen Ibrahim Kallah

Thursday, September 4, 2008


Wannan hoton Marubuci Dk. Yusuf Adamu ne tare da Manazarci Farfesa Abdalla Uba Adamu a Maradi, Jamhuriyar Nijar.

SANARWAR BUDEWA

Ina farin cikin samar da wannan dandali na Marubutan Hausa. Kamar yadda aka nuna a sama, manufar wannan dandali shi ne a samar da bayanai da suka shafi tarihi da rayuwar Marubutan Hausa da rubuce-rubucensu. Saboda haka, zan yi amfani da wannan dama domin rokon Marubutan Hausa duk inda suke a duniya da su taimaka su aiko mun da tarihinsu da duk wani bayani da suke so duniya ta sani a game da su da kuma jerin sunayen littattafansu don bugawa. Za a iya aikowa da wadannan bayanai ta email dina watau yusufadamu2000@yahoo.com Ina rokon Marubuta su ba mu cikakken goyon baya. Na gode.

Dk. Yusuf M Adamu