Sunday, September 7, 2008

AUWALU YUSUFU HAMZA










An haifi Auwalu Yusufu Hamza a 1959 a Nguru Jihar Yobe, kodayake, iyayensa mutanen Utai ne cikin Karamar Hukumar Wudil, Jihar Kano. Ya yi karatunsa a Jamiár New York, Amurka inda ya yi digiri a fanning Nazarin Al’adu (Anthropology). Bayan ya dawo Nijeriya ya fara aiki a History and Culture Bureau ta Jihar Kano inda ya yi jagorar kafa ANA reshen jihar Kano. Ya bar History and Culture Bureau a 1997. Daga baya ya yi aiki a CRD watau Center for Research da Documentation Kano da kuma SLPG Dutse Jihar Jigawa. Shine jamiín da ya dage wajen tabbatar da cewa an samu reshen ANA a Kano lokaci yana aiki a HCB, kokarinsa ne ya jawo aka fara kafa ANA Kano a 1992, wadda ba ta je koína ba ta rushe, da aka sake kokarin sake kafa ta a 1995, ya bada gudunmuwa babba daga nan kuma ANA Kano ta ci gaba da wanzuwa har yau. Ya taba zama Shugaban ANA Kano daga 1998-2000. Saboda tsarin ayyukansa ya samu zagayawa kauyukan arewancin arewar Nijeriya kuma rubuce-rubucensa na nuni da yadda rayuwa take a kauyukan kasar Hausa. Yana rubutu da Hausa da kuma Turanci.




Litattafansa na Hausa sune:
Gidan Haya
‘Yarkwatano

Littattafansa na Turanci sune:
Love Path
A Question of Marriage
Open Courts
Citizens Parade

No comments: