Wednesday, May 20, 2009

HIRA DA YARON MALAM

Daga Maje El-Hajeej <sirrinsu@yahoo. com>


Nine Bajakaden Abubakar Imam. Cewar Yaron Malam. Tun lokaci da shahararren marubucin da a yau duniyar hausawa ke girmamawa a matsayin kakan marubuta ya amsa kira zuwa ga mahaliccinsa, manazarta suka dukufa domin zurfafa nazarin gano ko wanene zai gaji shi marigayin, tare da rike alkalaminsa ga ci gaba da assasa yanayi da kuma salonsa na imamantar da labari zuwa yadda zai dace da Hausawa da kuma al’adunsu. Musamman ma ko domin dinbim amfanin da a yau littattafansa ke dasu ga dalibai sakamakon sanya su da ake yi a manhajar karatu, da kuma zama tushe da suke yi na fara koyon karatu ga mafi yawancin garuruwan Hausawa.

Duk da dai wannan bakin gumurzu ne, wanda sai an samu sadauki mai akwatin siddabaru, ko kuma yakau dan mayakiya da zasu ja tunga, su kuma yi shahada, sannan su fara fafatawa suyi gumu gami da artabu tamkar a tsibirin Bamuda da yahudu badda musumi. Domin ba aiki ne na mata ba, ballantana gimbiya Assadatu ko Bajakadiya ko kuma Mayakiya suyi hargagagin farawa. Amma Abdullahi Mukhtar da ake yiwa lakabi da Yaron Malam, ya sanya sulke tare da daura damarar karbar wannan garkuwa ta Imam kamar yadda ya bayyanawa wakilinmu Maje El-Hajeej Hotoro.

(An yi wannan tattaunawa da shine a watan Janairun 2007)

Zamu fara da jin tarihinka. Sunana Abdullahi Mukhtar Yaron Malam, an kuma haife ni a 1976 a unguwar Fagge dake karamar hukumar Fagge Kano. Na kuma yi karatun firamare na a Fagge Special daga 1984 zuwa 1988. Inda na karasa karatun firamarena a Gama Sabuwa saboda komawa can da muka yi. Dagan nan kuma ban samu damar ci gaba da karatuna ba, sai aka kaini makarantar allo a garin Hadeja. Wacce ban dade ba aka dawo dani, sakamakon rashin lafiya da na yi, inda na ci gaba da karatun allo. Kafin daga baya na shiga makarantar koyom larabci ta Aliyu Bn Abu Thalib, wacce daga baya aka mayar da ita Umar Bn Khattab dake Gyadi-gyadI a nan Kano daga 1994 zuwa 1999. Lokaci guda kuma ina mai ci gaba da halartar karatun azure. Na sake shiga makarantar koyon larabci ta Rasulul Akram, bayan na kamala na tafi Irshadul Umma Islamic College ta Shahuci da ake kira da Aliya daga 2001 zuwa 2004. Wanda a halin yanzu ina jami’ar Bayero, inda nake karanta aikin jarida. Tare da dan hadawa da kasuwanci.

Shin ko a wacce shekara ka fara rubutu, kuma ko menene ya dauki hankalinka har ka shigo fagen?
Alal hakika zan iya cewa tun farko na taso ne da sha’awar rubuce-rubuce, domin tun ina firamare na kan dauki takarda nayi ta kwafar littafin Baba da Inna da kuma Iliya dan mai karfi a cikin littattafan makaranta na. Sannan kuma ni dama makaranci ne na littattafan labaran Larabci da Hausa. Kamar irinsu Magana Jar ice, Yawon Duniyar Haji Baba, Labaran Da da na Yanzu, da sauransu. Domin ko a lokacin da na ke makarantar Allo, ragowar ’yan uwana almajirai kan zagaye ni na rika basu labarin wani littafi dana karanta. Na fara fitar da littafina na farko ne a 1999 wanda na addini ne mai suna Hukunce-hukuncen Azumi da Addu’o’in Watan Ramadan. Sai kuma Hukunce-hukuncen Jinin Haila, amma ban fitar dashi ba, sai bayan da na fitar da littafina mai suna kissoshin Ahlul Baiti. Dagan an kuma sai na fitar da Bajakade da kuma sirrin aure da ma’aurata, wadanda sune litattafan da suka zama sanadiyyar aka anni a duniyar marubuta.

A halin yanzu ko littattafanka sun kai nawa?
Zuwa yanzu na samu nasarar rubuta littattafai da dama kamar, Bajakade, Mayakiya, Bakin gumurzu, Gimbiya Assadatu, Artabu, Fafatawa, Gumu, Tsiburin Bamuda, Sadauki mai akwatin siddabaru, Tunga, Shahada, Bajakadiya, ‘Yar mai ganye, Yakau dan mayakiya da kuma Yahudu badda Musulmi da kuma na addini da dama.

Ko da wane irin salo kake amfani a rubutunka?.
Salon rubutuna sune salon jarumta, abin dariya, soyayya da kuma hikimar Magana. Jigo kuma shine karfafa akidar addinin musulunci, tsayar da adalci da kuma kyautata zamantakewa tsakanin al’ummar musulmi da kuma wadanda ba musulmi ba.

Mafi yawancin irn wadannan littattafai da suke dauke da abubuwan da ka rubuta akan samu fassarowa ake daga wasu littattafai, shin naka ma fassara ne ko kuma kirkirowa kake yi?
Maganar gaskiya ina kirkirar labari na ne, kuma mafi yawanci duk wanda ya dauko wani littafi ya fassara, sai an samu wasu sun daga sun ce ga daga inda ya fassaro. Amma ni babu wanda zai daga littattafaina yace ga daga inda na fassaro. Sai dai ina karance-karance kamar yadda na fada domin kaifafa basirar da Allah Ya yi min, wanda dama ita baiwa ce, amma ilimi, bincike da kuma tambaya akan abin day a shigewa mutum duhu, sune abincin basira. Sannan juya ilimi daga wani harshen zuwa wani ba laifi bane, matukar anyi hakan ta halattacciyar hanya ba satar fasaha ba.

Ko me zaka iya cewa dangane da kalaman Dakta Malumfashi da kuma na Farfesa Abdallah da suka bayyana cewa nan gaba zaka iya gadar Marigayi Abubakar Imam a fagen rubutu?
Wannan ba a bin mamaki bane idan aka yi la’akari da yanayi da kuma salonsa na ban dariya da dabarun zaman duniya da kuma hikimar Magana. Kana kuma yana gina labarin san e akan sigar zamanin da, sannan wani lokaci yak an jefa soyayya. To idan akayi la’akari da yanayin rubuce-rubucena salon da nake bi kenan. Kumai an matukar samun karfafawa akan wannan salon rubutu nawa, domin farfesa Abdallah yak an kira ni da sabon Abubakar Imam. Sannan musamman ya zaunar dani ya bani labarin dabarun da marigayin ke bi a rubutunsa. Sannan akwai Malam B.K Zariya wanda sunyi zamani da Marigayi Imam, shima takanas yakan kirani ya zaunar dani ya sanar dani tarihin yadda rayuwar Abubakar Imam ta kasance, harma yakan kirani da marigayi Imam.

Shin ko akwai wata kyauta da makarantanka suka taba yi maka wacce ba zaka taba mantawa da ita ba?.
Akwai wata a Bauchi da ta taba yi min kyautar Alqur’ani mai girma, wacce a gaskiya bazan manta da wannan kyautar ba. Sannan kuma masoya daga wurare daban-daban, suna yi min fatan alheri wanda wannan ma babbar kyauta ce, dab a zan manta da ita ba.

Ko a wane irin yanayi ka fi son yin rubutu?
Ina yin rubutu a kowane irin yanayi, amma nafi jin dadin yanayin bayan sallar asuba. Amma a yanzu na dauki wani salo nana yin rubutu a bakin ruwa, ko cikin daji mai bishiyu da kuma ciyayi, ko wajen gari kamar yadda Abubakar Imam ya yi.

Ko shin a matsayinka na dan kasuwa yaya kake hada harkar rubutu da kuma kasuwanci lokaci guda?.
Ai shi rubutu baya hana marubuci yi wasu abubuwan yau da kullum. Misali idan ka dauki marigayi Imam malamin malakaranta ne kuma marubuci lokaci guda. Sannan daga bisani ya zama Editan wata jarida, wanda a wannan lokacin babban aiki ne saboda karancin kayan aiki. Haka ma a yau zaka samu marubuta suna kuma wasu abubuwa na daban, ciki hard a sojoji da ‘yan sanda da sauran ayyukan gwamnati ko kuma na kamfani kuma wannan baya hana su rubutu.

Da kayi maganar kasuwanci sai ka tuno da korafin da wasu marubuta ke yi na matsalar ‘yan kasuwa, wajen rashin sakar musu kudadensu da wuri bayan an sayar da kayansu.?
Lallai kam wannan matsala ce da muka dade muna kuka da ita, amma yanzu alhamduLillahi al’amura sun fara kyautata, domin zaka samu mud a kanmu marubutan muna yabon wasu ‘yan kasuwar da kokarin bayar da kudI akan kari. Su kuma wadanda ake samun jinkirin sun dauki alwashin magance hakan. Sannan kuma kungiyar masu littattafai da kuma ‘yan kasuwa, suna aiki tukuru wajen ganin ta magance wannan matsala. Mu kara hakuri nan ba jimawa ba, komai zai zama tarihi Insha Allahu.

Kwanakin baya kungiyar marubuta ta kasa reshen jihar Kano (ANA) ta jagoranci marubutan Hausa wata tafiya zuwa kasar Nijar. Kasancewar kana cikin shugabannin wannan kungiya, ko wadanne matsaloli da kuma nasarori kuka samu yayin wannan tafiya.?
Makasudin wannan tafiya shine ziyara da kuma taron karawa juna sani tsakanin marubutan Nijeriya da kuma na waccan kasa. Kana kuma da yin bincike akan yanayin zamantakewa da al’adunsu domin samun karin gogewa ga marubutanmu na nan. Matsala kadai da muka samu ita ce ta motarmu da ta lalace, wanda hakan ya tilasta mana yin amfani da guzurinmu domin kara hayar wata motar da ta karasa dam u can. Mun kuma samu nasarori sosai musamman ma na karawa juna sani, sannan ga kuma ziyarar muhimman wurare da muka yi, sun kuma karrama mu sosai domin hidimomi da suka yi man na tsaro da kuma makwanci. Sannan kuma mun fa’idantu matuka gaya , basirarmu ta kara fadada, wanda dama masu hikima sunce tafiya mabudin ilimi.

TA'AZIYYAR YARON MALAM

Allah ya yi wa Abdullahi Muktar Yaron Malam rasuwa ranar Lahadi 17 ga Mayu 2009 da misalin sha biyu na rana, a dakin Karatu na Muratala Muhammad dake birnin Kano. Ya rasu ya bar mata daya da diya uku. Fitaccen marubuci, shugaban Brigade Authors Forum (BAF) kuma jami'i a Kungiyar Marubuta ta Nigeria (ANA) reshen Jihar Kano, Yaron Malam marubuci ne ingarma wanda ya bada muhimmiyar gudunmuwa wurin ci gaban adabin Hausa. Yaron Malam kuma mawallafi ne kuma mai sayar da littattafai. Mun yi babban rashi. Allah ya jikan Yaron Malam ya gafarta masa amin.


Dr Yusuf M Adamu
Shugaban ANA Kano

Dannan wannan rariyar likau don karanta takaitaccen tarihin Abdullahi Muktar Yaron Malam: http://marubutanhausa.blogspot.com/2009/02/abdullahi-mukhtar-yaron-malam.html

Saturday, May 2, 2009

KABIRU YUSUF ANKA



An haifi Kabiru Yusuf Fagge (anka), a unguwar Fagge. Ya fara karatun Alkur'ani a makarantun allo, da Islamiyya ta Sabilul Rashad da ke Gyadi-gyadi da Mukhtariyya Islamiyya da ke unguwar Fagge da kuma Thimarul Kur'an (bangaren dare) ya sami saukar Kur'ani, da karanta sauran littattafan addini.
Ya fara karatun Firamare a Kurna Special Primary School da sakandire a JSS Kurna,  Sai Jami'ar Bayero inda ya sami shaidar Diploma a bangaren aikin jarida (Mass Communication), sannan kuma ya samu shaidar karatun Diploma a bangaren Statistics, da kuma Diploma a na'ura mai kwakwalwa (Computer) a makarantun: Online Computer da kuma Hands-On Computer Institute inda ya karanci (Desktop Publishing da Data Processing and Maintenance), ya karanci Diploma in Film and Television Production a Northwest University, Kano, a wannan shekara ta 2020 yana Jami'ar Bayero, yana karantar Hausa.
Ya sami kwarewa a fannin sarrafa na'ura mai kwakwalwa musamman a bangaren zane da bugu (design graphics and typing).
Ya buga littattafai, jaridu da mujallu masu yawa a bugun kwamfiyuta, ya kuma tsara shafukan mujallu da jaridu da kuma tsara bangwayen littattafai da yawa.
Ya yi rubuce-rubuce a jaridu da mujallu  kamar haka:-
Wakiliya -(mujallar Marubuta) - a matsayin mataimakin Edita.
Inuwar Marubuta -(mujallar Marubuta) - marubuci na musamman
Suda -(mujallar 'yan fim) - marubuci
Kwallon Kafa -(mujallar labarun wasanni) -mataimakin Edita.
Muryar 'Yanci -(jaridar labaran karamar hukumar Fagge) -Edita
Masoya -(mujallar labaran rayuwa da soyayya) - Edita
Kakaki -(mujallar kare ra'ayin karamar hukumar Fagge) -Edita
Haka ya yi rubuce-rubuce da dama a jaridu da mujallu na kasar nan. Ya wallafa littattafai da dama.

YADDA YA SAMI KANSA A RUBUCE-RUBUCE
Tun a aji hudu na firamare ya zama mai iya karance-karancen littattafan Hausa da Jaridu, shi da wani abokin karatu mai suna Abdulhamid Muhammad Al'ansari wanda asalinsa Kwara ne, da shi suke siyo littattafan da jaridu suna karantawa, don haka sai ya fara karanta MAGANA JARI CE a ajinsu, daga nan ya sami kan sa a rubuce-rubuce.
LITTAFAN DA YA RUBUTA
Ya rubuta littattafai da dama, amma wadanda ya fitar guda goma bangaren hikaya:
1. Karfin Hali
2. Shure-shure
3. Ninkaya
4. Alwashi
5. Bilkisu
6. Firgita Samari...
7. Rayya
8. 'Yanmata
9. Kushewar Badi
10. Launin So

Sai kuma littattafan ilimi na koyarwa
The Boy Who Cried Wolf (anthology of short stories)
Dabarun Rubuta Kagaggun Labarai
Mu Koyi Karatu 1,2,3,4,5
Tatsuniyoyi Da Labarun Gargajiya

Sai kuma littafan WASAN KWAIKWAYO:
1. KOWA YA YI DA KYAU
2. TUTAR BABU
3. KURMAN AMO

Sai kuma littattafan da suka shafi bandariya da sauran hikaya
1. Mu Sha Dariya
2. Kai Ma Ka Dara
3. Abokin Dariya
4. Malamin Ban Dariya
5. A Ba Su Dariya
6. Gidan Dariya
7. Zunbuli Kakan Marowata

Sannan akwai littattafan da suka shafi koyar da yara kanana karatu da rubutu kamar:
1. Standard Dictionary
2. The Boy Who Cried Wolf
3. Alphabet for Kids
4. Mathematics for Kids
5. Successful Drawing Book for Children
Da sauransu

FINA-FINAI
Ninkaya, 
Sulusi, 
Sakin Aure, 
Hakkin Miji, 
Aure Ibada Ne, 
Sallamar Bankwana, 
Sharri Kayan Kwalba, 
Karshenki, 
Matar Waye?, 
Mahaifiyarmu, 
Wa Ya Kasheta?, 
Dan Garba, 
Sarkin Barayi, 
Sarkin Aska, 
Kwalba
Wace Ce Ni?
Goyon Kaka

Series
'Ya'yanmu, 
Mu Sha Dariya, 
Butulcin Zuci


Yana da aure da 'ya'ya