An haifi Kabiru Yusuf Fagge (anka), a unguwar Fagge. Ya fara karatun Alkur'ani a makarantun allo, da Islamiyya ta Sabilul Rashad da ke Gyadi-gyadi da Mukhtariyya Islamiyya da ke unguwar Fagge da kuma Thimarul Kur'an (bangaren dare) ya sami saukar Kur'ani, da karanta sauran littattafan addini.
Ya fara karatun Firamare a Kurna Special Primary School da sakandire a JSS Kurna, Sai Jami'ar Bayero inda ya sami shaidar Diploma a bangaren aikin jarida (Mass Communication), sannan kuma ya samu shaidar karatun Diploma a bangaren Statistics, da kuma Diploma a na'ura mai kwakwalwa (Computer) a makarantun: Online Computer da kuma Hands-On Computer Institute inda ya karanci (Desktop Publishing da Data Processing and Maintenance), ya karanci Diploma in Film and Television Production a Northwest University, Kano, a wannan shekara ta 2020 yana Jami'ar Bayero, yana karantar Hausa.
Ya sami kwarewa a fannin sarrafa na'ura mai kwakwalwa musamman a bangaren zane da bugu (design graphics and typing).
Ya buga littattafai, jaridu da mujallu masu yawa a bugun kwamfiyuta, ya kuma tsara shafukan mujallu da jaridu da kuma tsara bangwayen littattafai da yawa.
Ya yi rubuce-rubuce a jaridu da mujallu kamar haka:-
Wakiliya -(mujallar Marubuta) - a matsayin mataimakin Edita.
Inuwar Marubuta -(mujallar Marubuta) - marubuci na musamman
Suda -(mujallar 'yan fim) - marubuci
Kwallon Kafa -(mujallar labarun wasanni) -mataimakin Edita.
Muryar 'Yanci -(jaridar labaran karamar hukumar Fagge) -Edita
Masoya -(mujallar labaran rayuwa da soyayya) - Edita
Kakaki -(mujallar kare ra'ayin karamar hukumar Fagge) -Edita
Haka ya yi rubuce-rubuce da dama a jaridu da mujallu na kasar nan. Ya wallafa littattafai da dama.
YADDA YA SAMI KANSA A RUBUCE-RUBUCE
Tun a aji hudu na firamare ya zama mai iya karance-karancen littattafan Hausa da Jaridu, shi da wani abokin karatu mai suna Abdulhamid Muhammad Al'ansari wanda asalinsa Kwara ne, da shi suke siyo littattafan da jaridu suna karantawa, don haka sai ya fara karanta MAGANA JARI CE a ajinsu, daga nan ya sami kan sa a rubuce-rubuce.
LITTAFAN DA YA RUBUTA
Ya rubuta littattafai da dama, amma wadanda ya fitar guda goma bangaren hikaya:
1. Karfin Hali
2. Shure-shure
3. Ninkaya
4. Alwashi
5. Bilkisu
6. Firgita Samari...
7. Rayya
8. 'Yanmata
9. Kushewar Badi
10. Launin So
Sai kuma littattafan ilimi na koyarwa
• The Boy Who Cried Wolf (anthology of short stories)
• Dabarun Rubuta Kagaggun Labarai
• Mu Koyi Karatu 1,2,3,4,5
• Tatsuniyoyi Da Labarun Gargajiya
Sai kuma littafan WASAN KWAIKWAYO:
1. KOWA YA YI DA KYAU
2. TUTAR BABU
3. KURMAN AMO
Sai kuma littattafan da suka shafi bandariya da sauran hikaya
1. Mu Sha Dariya
2. Kai Ma Ka Dara
3. Abokin Dariya
4. Malamin Ban Dariya
5. A Ba Su Dariya
6. Gidan Dariya
7. Zunbuli Kakan Marowata
Sannan akwai littattafan da suka shafi koyar da yara kanana karatu da rubutu kamar:
1. Standard Dictionary
2. The Boy Who Cried Wolf
3. Alphabet for Kids
4. Mathematics for Kids
5. Successful Drawing Book for Children
Da sauransu
FINA-FINAI
• Ninkaya,
• Sulusi,
• Sakin Aure,
• Hakkin Miji,
• Aure Ibada Ne,
• Sallamar Bankwana,
• Sharri Kayan Kwalba,
• Karshenki,
• Matar Waye?,
• Mahaifiyarmu,
• Wa Ya Kasheta?,
• Dan Garba,
• Sarkin Barayi,
• Sarkin Aska,
• Kwalba
• Wace Ce Ni?
• Goyon Kaka
Series
• 'Ya'yanmu,
• Mu Sha Dariya,
• Butulcin Zuci
Yana da aure da 'ya'ya
6 comments:
Dear Dr. Adamu, I have been following your blog for some time now. Just wondering if you can recommend some Hausa authors? Thanks very much.
Mallam na ga abnda ka rubuta, ne ma na ye karatu na a Kurna ama 1979 na fara.
I enjoyed reading your story, I also went to Kurna Primary 1979 to 82. Kurna is another world from where I am today. Again thank you and keep writing.
Hey Mr. Anka its me Izzah am in Germany, with friends just sarching for Hausa writing thn i meet u on this site am glad to see u on this stage n happy pls my regardz to all Gizo Staff
Allah yakara maka baiwar rubuce rubucen dakasa agaba daga yayenka Murtala Inuwa daga Sudan
Gaskiya saidai san barka idan akayi da la'akarin yadda harkar kasuwancin ka yashara wajen wallafa littafai wanda akowanne yanayi dazamani yazo dashi ba abarka abayaba fatana anan Allah yakara basira Ameen
Post a Comment