Sunday, September 7, 2008

ADO AHMAD GIDAN DABINOAn haifi Ado Ahmad Gidan Dabino a Danbagina Karamar Hukumar Dawakin Kudu a shekarar 1964, ya yi karatun allo a Zangon Barebari. Bai samu damar yin karatun boko ba sai da ya kai shekara ashirin, sannan ya fara zuwa makarantar yaki da jahilci ta masallachi, watau makarantar da aka fi sani a Kano da makarantar Baban Ladi,daga nan ya yi karatun Sakandare a GSS Warure inda ya samu SSCE a 1990. Daga nan ya yi kwas na shekara guda akan karatun makafi da koyon aikin kafinta, A shekarar 2005 kuma ya sami diploma akan aikin sadarwa daga jamiár Bayero ta Kano. Ado Ahmad na daya daga cikin fitattun marubutan Hausa na zamani kuma littafinsa mai suna In da So da Kauna na daya daga cikin fitattun littattafan Hausa na kowane zamani. Ya rike mukamai da dama a Kungiyoyin marubuta, shi ne shugaban Kungiya Marubuta ta Raina Kama, ya taba zama Mataimakin shugabna ANA reshen Kano, ya zamar mata maáji kafin ya zama shugabanta tun 2006 zuwa yau. Ya taba zama Edita na FIM magazine kasancewar daya daga cikin wadanda suka kafata a 1999. Shi ne mawallafin Mumtaz kuma shugaba/daraktan gudanawarwa na Gidan Dabino International Nigeria Limited. Ya gabatar da makalu a manyan tarrurruka na karawa juna sani a jami'oí daban daban na Nijeriya. Dan wasan Hausa ne, dan jarida kuma mawallafi. Litattatafansa da suka fito sune:

In Da So da Kauna 1 da 2 (1991)
Hattara Dai Masoya 1 & 2, (1993)
Masoyan Zamani 1& 2, (1993)
Wani Hani Ga Allah 1 & 2, (1995)
Duniya Sai Sannu (1996)
Kaico (1997)
Sarkin Ban Kano (2004) tare da Sani Yusuf Ayagi

An fassara wasu dag cikin litattafansa kamar haka:

The Soul of My Heart (Translation of In Da so Da Kauna), (1994)
Nemesis (Translation of Masoyan Zamani) 1996

Ana iya samun Karin bayani game da rubuce-rubucensa a http://www.gidandabino.blogspot.com/
Email address: gidandabino@yahoo.com

No comments: