Sunday, September 7, 2008

Sakwannin Ba da Kwarin Gwiwa

Wadannan sakwanni ne na ba da kwarin gwiwa da na fara samu daga marubuta da makaranta. Na ji dadinsu kuna ina fatan wannan ya zama alama ta irin goyon bayan da wannan aiki zai samu. Ba aika na ne ni kadai ba, aikinmu ne gaba daya kuma muna rokon kowa ya ba da gudunmuwarsa.

“Salam, Madalla da wannan gagarimin aiki naka,Allah ya saka da alheri amadadin marubuta,duk da dai mu 'yan kallo ne amma abin yayi dai dai.da fatan za'a sha ruwa lafiya amin
Daga Sunusi Bature Dawakin Tofa,Freedom (FM) Kano

“Tare da sallama. Malam barka da wannan gagarumin kokari, sai dai mu ce (marubuta) Allah ya saka da alkairi. Tambaya daya ce, shin ba za a iya shiga cikin dandalin kai tsaye ba, a aika da sakon? Kuma shafin ya tsaya ne a iya tarihin marubuta, ko kuma akwai wasu bayanai na al'amuran yau da kullum da suka shafe.Da fatan an sha ruwa lafiya, Allah ya ba mu lada da falolin da ke cikin wannan wata mai alfarma, amin summa amin.,
Daga Kabir Anka

"Wannan ba karamin kokari ka yi ba don adana tarihi da hotunan mutane masu basira da fasaha a waje daya yadda masu bincike za su sami sauken tattara bayanan da suke nema game da marubutan ba. Allah ya yi jagora, amin”.
Daga Ado Ahmad Gidan Dabino

“Assalamu Alaikum, Ranka Ya Dade!!! Barka da wannan babban kokari, hakika wannan aiki ne wanda ya kasance abin yabawa da kuma jinjinawa a gareka, domin samun irin ka a cikin al’umma ba su da yawa. Ka kawo wani babban ci gaba wanda ba a taba samun irin sa ba, sannan kuma ka kawo hanyar da duk duniya zata san Marubutan Adabi da kuma littattafan Adabi wanda a da sai wane da wane ne suke samun damar sanin su. Wannan wata hanya ce wacce su kansu Marubutan Adabi za su dage dantse wajen ganin sun inganta aikinsu kasancewar wannan wata babbar allura ce wacce ta fi ta sojoji sa kaimi da zagewa, tun da a halin yanzu duk duniya ce ta ke kallon su.

“A karshe kuma ina ganin ya kamata a rika hadawa da email din Marubuci, don wasu basu da blog wanda za a samu bayaninsu a ciki. Bayan haka, idan da hali ina ga ya kamata duk littafin da aka sa sunan sa to a bude masa shafi yadda idan har mai bincike yana bukatar karantawa zai iya karantawa ta cikin wannan fage. Jinjina mai yawa da wannan babban Jihadi, Allah Ya biya ka da gidan Aljannah. Da fatan Allah Ya sa ‘yan baya mu yi koyi!!!”

Daga Mohd Mohd Assadiq


“Masha Allah...muna nan tafe...Allah ya bar girma, mu ci gaba da samu daga fasaha da ilimunku.... A sha ruwa lafiya.”
Daga Umar Mannoter

Salam a gaskiya wannan abu ne da ya zama abin alfahari gare mu hausawa da ma harshen hausa, wannan na nuna mana cewa zuwa wani lokaci za a kara samun ci gaba a wannan harshe namu na hausa.mun godeDAG IBRAHIM YARO D/TOFA MEDIA TRUST LIMITED ABUJA[JARIDAR AMINYA]

1 comment:

Anonymous said...

salam a gaskiya wannan abu ne da ya zama abin alfahari gare mu hausawa da ma harshen hausa, wannan na nuna mana cewa zuwa wani lokaci za a kara samun ci gaba a wannan harshe namu na hausa.mun gode
DAG IBRAHIM YARO D/TOFA MEDIA TRUST LIMITED ABUJA[JARIDAR AMINYA]