Monday, September 8, 2008

HADI ABDULLAHI ALKANCI


Fitaccen marubucin Wasan Kwaikwayo na Hausa Hadi Abdullahi Alkanci, an haife shi ranar 1 ga janairu 1957 at Alkanci, Birnin Sakkwato. Ya yi karatu a Kofar Marke Nizzamiyya school (yanzu ana cewa makarantar Alhaji Alhaji Model Primary School, Sokoto). A shekarar 1973 ya tafi Sultan Abubakar College Sokoto, inda y agama da Grade II Teacher a 1977. Ya yi aiki a sashen Ilmi na Karamar Hukumar Sakkwato, ya koyar a Army Children School Sokoto daga 1977-78. Daga nan ya tafi Staff Training Centre (yanzu College of Administration, Sokoto) inda ya yi satifiket kan Fassaradaga 1978-79. Ya yi aiki a Rima Radio Sokoto daga nan ya yi ritaya ya fara kasuwanci, a wannan lokaci ya tan tabawa N.T.A Lagos, aiki inda yak e gabatar da wani shiri mai suna "WAZOBIA" ya kuma dan taba aikin karatun labarum duniya duk daga 1981-82. Ya zama daya daga cikin manyan daraktocin ALKANCI ENTERPRISE. A wannan lokaci ya samu damar ziyartar kasashen duniya da dama. A shekarar 1986 ne ya bar harkar kasuwanci ya dawo ya dukufa wurin harkar rubutu da aikin jarida. Malam hadi Alkanci ya gabatar da makalu iri daban daban a tarurruka na marubuta da adabi a jamióí daban da ban na kasar nan kuma fitaccen marubucin wasan kwaikwayo ne na Hausa. A shekarar 1981 ne aka buga littafinsa na farko mai suna Soyayya Ta Fi Kudi wanda sashen aládu na Maáikatar Aládu ta tarayya ta buga. Ya rubuta littattafai da dama wasu daga cikinsu sun hada da:
Soyayya Ta Fi Kudi (Wasan Kwaikwayo)
Harsashin Kasa
Karatun A cikkin Hotona 1
Shin So Gaskiya Ne?
Zaben Allah
Jagora Ga Mai Aikin Hajji
Bayansu akwai litattafai da dama day a rubuta wadanda ba a buga ba. Mamba ne na ANA Sokoto. Malam Hadi ya bada gdunmuwa sosai wurin habaka adabin Hausa musamman a Sakkwato kuma duk wanda ya sanshi a sakkwato a yau to a marubuci ya san shi. A halin yanzu shi n eke buga mujallar Sahihiya a Sakkwato.

2 comments:

SK Usman said...

Inna lillahi, wa inna ilahirrajiun! Yanzu ne na sami labarin rasuwar wannan bawan Allah a dandalinmu na fina-finan hausa. Allah Ya jikansa, kuma Ya albarkaci abin da bari baya.
A gaskiya rasuwarsa ba karamin rashi bane. Allah Yasa ya huta.

Anonymous said...

Allahu Akbar!Allahu Akbar!Allahu Akbar!
Allah kayi gafara ga Hadi Abdullahi Alkanci.
Babu shakka Jahar Sakkwato munyi babban rashi na haziki,gwarzo,zarumi,sadauki,mai kishi da burin ganin wannan Jaha da Najeriya sun ci gaba.
Hakika,Hadi Abdullahi ya bada gagarumar gudunmawa ta fagen sadaukar da lokacinsa, dukiyarsa da karfinsa wajen bunkasa harkokin Addinin Musulumci, harshen Hausa da al"adar Malam Bahaushe.
Rasuwar Malam Hadi ta bar babban gibi a jahar Sakkwato da Najeriya baki daya,wanda muke ganin rufe wannan gibi yana da wahala a nan kusa'domin ya gina Marubuta da dama a wannan Jahar da ma sauran Jahohi.Fatar mu a nan shine,wannan kokari da yayi ya zama sanadin tsira a gareshi.
Karshe, na ke cewa,Allah Ya sa Aljanna ce makomar sa,da duk sauran Musulmin duniya. Allah Ya albarkaci zuriyarsa da ya bari. Mu kuma Allah Ya yi mana karshe na kwarai Ya sa Aljanna ce makomar mu.Amin.

Wassalam.
Daga;
Nasiru B.A Hassan,Sokoto
Marketing Manager,
SAHIHIYA PUBLICATIONS CENTRE,
SOKOTO.
08030484545
08097646967
e-mail- b_ahassan@yahoo.com