Thursday, September 11, 2008

BASHIR YAHUZA MALUMFASHI


An haifi Bashir Yahuza Malumfashi a ranar 15 ga watan Mayu na shekarar 1967 a garin Malumfashi, Jihar Katsina. Ya yi karatun firamare a Tunau Primary School, Unguwar Sodangi, Malumfashi, daga 1973 zuwa 1980. Daga nan ya wuce zuwa Government Day Secondary School, Malumfashi, daga 1981 zuwa 1986. Ya samu zuwa Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a (CAS, Zaria), daga shekarar 1987 zuwa 1989. Bai ci gaba da karatu ba saboda matsalar rashin lafiya da ta same shi, amma daga bisani ya shiga Kwalejin Horar da Jami'an 'Yan Sanda ta Kaduna (Police College, Kaduna), inda ya samu horo kan aikin 'yan sanda. Ya yi karatun Diploma a fannin Hikimar Koyar da Turanci (Diploma in Language Education, English) a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina. Haka kuma ya yi karatun Diploma kan ilimin sarrafa kalmomi (Diploma in Computer Data Processing) a wata makarantar Kwamfuta mai zaman kanta. Ya halarci kwasa-kwasai da tarukan kara wa juna ilimi a fannoni da dama. Ya fara aikin 'yan sanda ne a garin Dutsin-ma, Jihar Katsina, inda daga nan ya koma Kurfi, duk dai a Jihar Katsina. Daga bisani aka sake yi masa canjin wurin aiki zuwa Funtua, duk dai a Jihar Katsina. Ya samu canjin wurin aiki daga Funtua, aka mayar da ni zuwa Katsina. Daga nan ne aka mayar da shi aiki zuwa Abuja, inda na yi aiki a Babban Ofishin Binciken Laifuffuka na Hukumar 'Yan Sanda ta Kasa (Force Criminal Investigation Department), Area 10, Abuja. Mafi yawan aikinsa na 'yan sanda, ya yi shi ne a bangaren binciken laifuffuka da neman labarin sirri. A shekarar 2005 ne ya yi ritaya daga aikin 'yan sanda, bayan ya shafe shekaru 17 a kan aiki ke nan.

Ta bangaren harkar rubuce-rubuce kuwa, dama can shi mai sha'awar karance-karance da rubuce-rubuce ne. Ya fara rubutu tun yana aji uku a sakandare (1983), inda ya rubuta littafina na farko wanda ba a buga ba har yanzu. Sunan littafin Bak'i Da Fari, amma an karanta shi a Gidan Rediyon Nijeriya na Kaduna, a filinsu na Shafa Labari Shuni. Daga nan ya ci gaba da rubuce-rubuce, ana bugawa a jaridun Hausa da na Turanci, musamman ma Gaskiya Ta Fi Kwabo, Nasiha, Almizan, Katsina News Week, New Nigerian, Weekly Trust, da sauransu. Littafinsa na farko da aka buga kuma ya fito kasuwa shi ne Babban Tarko, wanda ya fito a cikin shekarar 1997. Sai kuma na biyu mai suna Bak'in Kishi, wanda ya fito kasuwa a shekarar 2003. Yakan rubuta wakoki na Hausa da na Turanci, wadanda ake yawan bugawa a jaridu. Littafina da ke kan hanyar fitowa, shi ne Zinatu Matar Gwamna, wanda aka dade ana tsakura shi a cikin jaridar Aminiya.

A tarihin rubuce-rubuce, ya shiga gasar rubutu da dama, inda a shekarar 1995 da 1996 na samu kyaututtuka daga gidan rediyon Muryar Nijeriya, Lagos, a sakamakon zuwa na biyu da mukalolina suka a yi a shekarun na jere. A 2004 ma ya samu nasarar zuwa na daya a gasar rubuta labarai da gidan rediyon BBC suka sanya, mai taken Labarina.

Bayan ya yi ritaya daga aiki 'yan sanda a shekarar 2005, sai ya fada aikin jarida, inda ya ci gaba da aiki da Mujallar Fim, wacce dama na dade yana aika masu rubuce-rubuce tun daga fitowarta. Ya rike mukamin Manajan Edita na mujallar, inda ya zauna Kano. Daga baya ya koma Kaduna, inda ya fara aiki da jaridar Turanci mai suna Public Agenda, a matsayin Editan Shafukan Adabi. A cikin shekarar 2006 ne ya bar wannan jarida, ya koma aiki a kamfanin Media Trust Limited, masu wallafa jaridun Daily Trust, Weekly Trust, Sunday Trust da kuma Aminiya. A jaridar Aminiya nake, inda shi ne Editan Shafukan Adabi da Nishadi na jaridar, duk da cewa yakan taimaka da rahotanni ga sauran jaridun Turanci na kamfanin, daga lokaci zuwa lokaci.
A halin yanzu, yana da aure da 'ya'yaye. Babban burinsa a duniya shi ne, na son ya ga harshen Hausa ya bunkasa, ya zama babba a duniya; kamar kuma yadda yake son ganin cewa ya zama babban marubuci, don ba da gudunmowata ga al'umma.

Littattafansa na Hausa da suka fito sune:

1- Babban Tarko - 1997.
2- Bakin Kishi - 2003

http://us.f431.mail.yahoo.com/ym/Compose?To=byahuza03@yahoo.com
GSM: 08020968758, 08065576011.

No comments: