Friday, September 5, 2008

YUSUF M. ADAMU


Yusuf Muhammad Adamu wanda yanzu aka fi sani da Yusuf Adamu na daya daga cikin fitattun marubutan Hausa na zamani. An haife shi a Katsina a shekarar 1968. Ya yi karatun firamare a Giginyu Primary School Kano daga 1974-1980. Ya tafi Sakandaren Gwamnati ta Koko cikin Jihar Kebbi daga 1980-1983 daga nan ya wuce Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati dake Zuru jihar Kebbi daga 1983-1985. A nan ne, ya fara rubuta littafinsa na farko watau Maza Gumbar Dutse. Ya samu shiga jamiár Usmanu Danfodiyo Sakkwato daga 1985-1990 inda ya samu digirinsa na farko a fanning Labarin Kasa (BSc Geography). A Jami’ar sakkwato ya rike mukamin Babban Magatarka na Kungiyar Hausa kuma Wazirin Sarkin Hausawa. Ya yi hidimar kasa (NYSC) a Dutsin Ma, inda ya koyar da Geography a Government Science Secondary School Dutsin Ma. A 1994 kuma ya samu digirinsa na biyu daga Jami’ar Ibadan. Ya fara aiki a Jamiár bayero ta Kano a 1995. A shekara ta 2004 kuma ya samu digirinsa na uku watau PhD a Geography. Yak ware ne a fanning Medical Geography. Yana da shaáwar gudanar da nazarce-nazarce akan lafiyar mata, kiwon lafiya, adabin Hausa na zamani da kuma fadadar birane.

Dk. Yusuf Adamu ya rike mukamai da dama a Kungiyoyin Marubuta. Ya taba zama shugaban Kungiyar Matasa Marubuta, ya kuma rike mukamin Magatakarda a Kungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA) reshen jihar Kano daga 1995-2000. Daga 2000-2006 ya zama Shugaban ANA Kano. Ya kuma taba zaman dan majalisar gudanawar na ANA ta kasa daga 1997-2001. Yana rubutu a harshen Hausa da kuma Turanci.

Litattafansa na Hausa na kirkira da aka buga sune:

Idan So Cuta Ne (1989)
Ummul-khairi (1995)
Maza Gumbar Dutse (2007)

Sauran litttafansa na Hausa (na kirkira) da ya gama amma ba a buga ba sun hada da:

Dukan Ruwa (1988)
Son Zuciya Bacinta (1989) Wasan Kwaikwayo
Gumakan Zamani (1992)
Zainab (yana kan aiki a kansa)

Littattafansa na Turanci kuma wadanda aka buga sune:
Butterfly and other poems (1995)
My first book of rhymes (1998)
Litters (2000)
Pregnant Skies: Anthology of 50 Nigerian poets (2003)
Landscapes of Reality (2007)
Animals in the Neighbourhood (2007)
Mazan Fara: ANA Zamfara Anthology (2008)
Kwaryar Kira (ANA Kano Hausa Anthology) tare da Ado Ahmad Gidan Dabino (2010)

Litattafan Ilmi da ya tace (co-editor)

Inequality in Nigeria: A Multidisciplinary Perspective (2003) tare da M.B. Shitu

Hausa Home Videos: Technology, Economy and Society (2003) tare da A.U. Adamu da U.F. Jibril

Corporate Survival, Competitiveness and Consumer Satisfaction in Nigerian Industries (2005) tare da M.S. Sagagi
Readings in Social Science Research (2006) tare da Habu Muhammed da K.I. Dandago

Introduction to Social Sciences (2008) tare da M.A. Yusuf da A.A. Adepoju

Email addresses: yusufadamu2000@yahoo.com /yusufadamu@gmail.com

1 comment:

Ahmad Abubakar Aliyu said...

har yanzu banga wakokin ahmad abubakar aliyu wanda suka kayatar musammam wakar nan matar dujal. daga Arabi Abubakar aliyu