Sunday, September 28, 2008

ZAKARIYA MUHAMMAD SARKI


An haifi Zakariyya Muhammad Sarki, a garin Kazaure ta Jihar Jigawa a shekarar 1976. Bayan karatun Muhammadiya, ya yi karatun Firamare da na karamar Sikandire a Kudu Central Primary da kuma Sikandiren Gwamnati da ke Kazaure a in da ya kamala a shekarar 1991. A lokacin ne kuma sha’awar rubuce-rubuce da karance-karance musamman na marubuta hausawa ya fara shiga zuciyarsa. Wannan ya sa ya zama mafi iya karatun littafi a cikin yan’uwansa dalibai. Duk da dai ba zai iya tuna labari daya da ya taba rubutawa ba a wancan lokaci, ya ‘saukewa’ yan ajinsu na firamare da na sikandire littatafai na Hausa irin su Magana Jari Ce, Iliya Dan Maikarfi, Da’u Fataken Dare, Dare Daya da dai sauran irin su sau bila adadin.Ya kamala karatun Sikandirensa a Sikandiren kimiyya ta gwamnati da ke Kafin Hausa a Jihar Jigawa a shekarar 1994. Ya samu shiga Makarantar Nazarin Addinin Musulunci da Shari’a ta Malam Aminu Kano (Legal), a nan ya samu shedar Diploma a kan Shari’a (Law) a shekarar 2003. Daganan ya wuce zuwa Jami’ar Bayero da ke Kano in da ya samu shedar samun Digiri na farko a fannin ilimin halayya da zamantakewar al’umma, (Sociology).. A yanzu haka kuma yana kan fara karatun Digirinsa na biyu a sabon zangon Karatu mai zuwa (2008/2009) a Jami’ar Bayero da ke Kano.

Zakariyya ya taba aikin kamfani a Kano da Legas a tsakanin shekarun 1995 zuwa 1999. Aikin da ya yi a Legas ya ba shi damar yin rubuce-rubuce a wasu fitattun jaridu na Kudancin Nijeriya kamar ‘The Punch’, ‘The Post Express’ da dai sauran irinsu. Haka kuma Zakariyya ya taba zama babban wakili (Bureau Chief) na Legas na kamfanin jaridar ‘The Shield Weekly’ da kuma Garkuwa da ke Kano. Ya taba zama wakilin Mujallar Fim a Kano. Hakanan kuma Marubuci na Musamman ga tsohuwar Mujallar ‘Mumtaz’ ta shahararren marubucin nan Ado Ahmad Gidan Dabino.

Zakariyya ya rubuta littattafai da kuma wakoki kirkirarru masu dama sai dai kuma ba’a taba buga ko daya daga ciki ba saboda wani shiri da yake da shi nan gaba (a shekarar 2009). Duk da haka a shekarar 2005 an juya littafinsa mai suna “Wuta a Masaka” zuwa fim mai taken “Wahami”, wanda darakta Ado Gidan Dabino ya bada Umarni. Zakariyya memba ne na Kungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA) reshen Jihar Kano. Ya na da mata da ya’ya biyu, kuma yanzu yana zaune a Kano.

Za a iya ziyartar blog din shi mai adireshi kamar haka http://www.zakariyyasarki.blogspot.com/
Ko kuma adireshin email : zakariyyasarki2005@yahoo.co.uk, zakariyyasarki@ymail.com
Lambobin Waya : 080-24388438, 064-893104, 064-317582.
** Mun buga wannan marubuci duk da cewa bai taba fidda littafi ba, bisa dalilai biyu, na farko dai mu kara masa kwarin gwiwa na biyu kuma tinda suna cikin na farko da suka turo ya samu wannan loto.

No comments: