Monday, September 8, 2008

BALARABA RAMAT YAKUBU


An haifi Balaraba Ramat Yakubu a Birnin Kano a shekarar 1958. Bayan neman ilminta na Islamiyya da na Boko daga shekarar 1962 zuwa 1980, Balaraba Ramat ta tsunduma wurin rubuce-rubuce masu koyar da zaman duniya da tunatarwa ga jamaá. A halin yanzu ita ce shugaba daraktar gudanarwa ta kamfanin Ramat General Enterprises da Mukaddas Nigeria Limited da kuma Ramat Productions Limited. Ta rike mukamai a kungiyoyin marubuta da dama, it ace mataimakiyar shugabar Raina Kama Writers Association, ta taba rike mukamin ma’aji a Kungiyar Marubuta ta Nijeriya reshen Jihar Kano (ANA Kano). A halin yanzu it ace shugabar Kallabi Writers Association. A halin yanzu tana da ýaýa biyar da jikoki uku, kuma ta rubuta litattafai har guda tara. Hajiya Balaraba ta samu kyaututtuka akan rubuce-rubucenta kamar kyautar taron Marubuta na Arewacin Nieriya da kuma kyautar adabi ta Engineer Kazaure. Bayan wannan masana na gida da wajen Nijeriya sun yi nazarce-nazarce da dama akan rubuce rubucenta. Kuma ta yi fice a Littattafanta sun hada da:

Budurwar Zuciya (1987)
Wa Zai Auri Jahila (1990)
Alhaki Kwikuyo
Badariyya
Wane Kare ne ba bare ba?
Matar Uba Jaraba
Ilmin Gishirin Zamani
Ina Sonsa Haka
Kyakkyawar Rayuwa

1 comment:

hadiza baba said...

ni ma'a buciyar karanta litafin hausa ce a lokacin da ina nigeria,amma a yanzu bana nigeria don Allah ko zan iya samun a net da kuma address din,ko kuma ta yaya zan iya samun sa a address dina kamar haka 329 tanjong katong road singapore.